Bai Kamata Atiku Da Buhari Su Tafi Kotu Ba – Sheikh Jingir

0
1407

Isah Ahmed Daga Jos

SHUGABAN Majalisar malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa bai kamata Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar da Shugaban kasa Muhammad Buhari su tafi kotu ba, kan zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar nan. Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.

Ya ce sam bai kamata Atiku da Shugaba Buhari  su tafi kotu  kan wannan zave da aka gudanar ba. Domin dukkansu kowa ya ce yana yin wannan takara ne  domin ya taimaka wajen gina Najeriya.

‘’Don haka ni a ganina bai kamata su shiga rigingimun shari’a ba. Su hada hanu wajen bunkasa tattalin arziqin Najeriya da ilmi da tsaro kamar yadda kowa ya yi alkawari. Domin dukkansu sun cewa Allah ne yake bayar da mulki.  Don haka su hada kai su baiwa marada kunya’’.

Shiekh  Jingir ya yi kira ga al’ummar Najeriya, su fito su zabi gwamnonin da zasu taimaki shugaban kasa Muhammad Buhari, a zaben da za a gudanar ranar asabar din nan.

Ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su yi sanyin gwiwa a wannan zaben gwamnoni da za a gudanar ba,  domin kada a fada gidan jiya.

‘’Don haka muna kira ga ‘yan Najeriya su fito su zabawa shugaban kasa gwamnoni nagari  da zasu taimaka masa,  don mun sha wuya da abokan adawa a wa’adin farko na mulkin Buhari’’.

Sheikh Jingir ya yaba da yadda aka gudanar da zaven shugaban kasa da ya gabata. Ya  ce Allah ya taimakemu a Najeriya, kan yadda  aka gudanar da wannan zabe domin   cigabanmu da ilminmu  da zaman lafiyarmu da adalcinmu ya bayyana a wannan zabe.

Ya ce babu shakka  jama’ar Najeriya  sun hadiye kwadayinsu sun fitata kasarsu  da zaman lafiyarta kan kudi a wannan zabe da aka gudanar. Don haka  wannan zabe ya kawowa Najeriya  daukaka.

Ya yi kira  Shugaba Buhari  ya cigaba da adalcin da aka san shi da shi kuma ya lura da miliyoyin ‘yan Najeriya da suka sadaukar da rayuwarsu suka zabe shi.

Ya kira ga shugaba Buhari ya dauki mutanen kirki da zasu taimaka masa,  kada ya dauki kara da kiyashi  da zasu kawo tarnaki irin wadanda suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here