Sanata Kabiru Gaya Ya Ziyarci Buhari Don Taya Shi Murna Lashe Zabe

0
1070
Daga Mustapha Imrana Abdullahi
SANATA mai wakiltar yankin Kano ta Kudu Kabiru Ibrahim Gaya tare da wata tawaga mai karfi sun ziyarci shugaban tarayyar Najeriya inda suka taya shi murnar lashe zabe.
A lokacin wannan ziyarar sanata Kabiru Gaya ya yaba  wa shugaba Buhari a game da irin ayyukan raya kasa da yake yi musamman aikin Layin Dogon da aka kammala a Kano.
A jawabinsa lokacin ziyarar shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Jihar Kano tare da dimbin al’ummar ta a matsayin wurin da yake alfahari da shi tun lokacin da ya shiga cikin harkokin siyasa a shekarar 2003. Inda ya bayyana Kano da cewa tana bashi gagarumin goyon baya tare da kuri’a tun ma lokacin da bai hau karagar Mulki ba.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da wata babbar tawagar mutanen Kano ta Kudu suka Kai Masa ziyara a fadar Gwamnati da ke Abuja. Ya tabbatar wa da tawagar cewa hakika mutane Jihar Kano na tare da shi a kowane yanayi.
Ya kuma bayyana gamsuwa da irin addu’o’i tare da goyon bayan da suke Nuna Masa a koda yaushe. Hakazalika ya kuma jinjina wa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya bisa irin goyon baya da taimakon da yake bashi, inda ya bayyana kasancewar Sanata Kabiru Gaya a matsayin shugaban kwamitin ayyuka a majalisar da cewa ya yi sanadiyyar samun nasarori da dama a Gwamnatinsa a cikin shekaru hudu.
Tun da farko a cikin jawabinsa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya Mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu wanda kuma shi ne ya jagoranci kakkarfar tawagar zuwa fadar shugaban kasa domin taya shugaban murnar lashe zaben da aka yi a satin da ya gabata ya roki shugaban da ya hanzarta kammala aikin Layin Dogo da ya taso daga Fatakwal zuwa Kano da kuma aikin fadada Layin Dogo na Kaduna zuwa Kano domin a samu saukin aiwatar da ayyukan sufuri wanda hakan zai sanya a samu sauki wajen lalacewar da tituna kan yi sakamakon manyan motocin da suke zirga zirga a kan titunan.
 Sanata Gaya ya kuma shaidawa shugaban kasa bukatar da ake da ita na Gina wata babbar Gadar sama a unguwar Mariri cikin Birnin Kano a yankin Kano ta tsakiya wanda hakan zai bayar da dama samun saukin salwantar rayukan da ake samu a lokacin kokarin jama’a na ketare hanyar domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Sanata Gaya ya kuma yi amfani da wannan damar inda ya godewa yan Nijeriya da suka zabi Jam’iyya Mai mulki da kuma al’ummar Kano ta Kudu da suka sake zabensa da gagarumin rinjaye a karo na hudu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here