Wata Kotu Ta Umarci Yan JTF Da Su Biya Tarar Diyar Naira 1,000,000

0
690

Musa Muhammad kutama Daga kalaba.

WATA Kotun taraiya dake Yenagoa a jihar Bayelsa karkashin jagorancin alkalin kotun maishari’a A.O Awogboro, a ranar juma’a 22 ga watan Fabreru ta umarci rundunar jami’an tsaro ta hadin gwiwa wato JTF na “Operation Delta Safe” da ta biya uwargida Yeibra Esigha diyyar naira
milyan daya sakamakon zargin tsare ta da suka yi ba bisa ka’ida ba.

A cikin takardar kara mai lamba FHC/YNG/CS/12019 da lauyan Esingha, Victor Gbafe ya gabatar na kwamandan rundunar operation Delta Safe, Riya Admiral A.O Suleiman bisa zargin take hakkin Dan Adam wanda hakan ya saba tsarin mulkin Najeriya.

Hakanan kuma an bukaci JTF din da ta gaggauta
sako wadda suke tsare da ita ba tare da wani jinkiri ba.

Takardar shigar da karar da lauyan wanda aka tsaren ba bisa ka’idar ba mai yawan shafi goma sha biyu ya bayyana cewar jami’an rundunar sun kama Yeibsa
Esingha ne ranar 31/12/2018 a garin Mbiama a yankin karamar hukumar Ahoada ns jihar ribas domin tursasa mijinta ya mika kansa gare su don
su bincike shi.

Da ta ke yanke hukunci, alkalin kotun mai shari’a Awogboro ta ce “kuskure
ne kama matar da ta ke shayarwa a tsare ta don hakan ya keta dokar ‘yan cin dan Adam saboda cin zarafi ne yin hakan ga kowane mutum a rayuwarsa.

Alkalin kotun ta ci gaba da cewa “matukar har hakan ya tabbata an saba doka
sashe na 35 na kundin tsarin mukin Najeriya na 1999.

Daga nan mai shari’ar ta bayar da umarnin a gaggauta sako matar ta dawo ta ci gaba da shayarwa ta, kana kada a kara kirawo matar domin zuwa ta yiwa JTF din wani bayani kuma ta rundunar tsaro ta hadin gwiwar operation Delta safe da ta nemi afuwar ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here