EFCC Ta Gurfanar Da Wani Dan Damfara A Gaban Kotu Dake Jihar Delta

0
699

Musa Muhammad Kutama Daga kalaba.

A YAYIN da al’ummar Abraka jihar Delta ke kukan lalacewar matasan su da
suka baci da harkar zamba ta kafar sadarwa, ofishin hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da wani Tayo Morawo da abokinsa a gaban babbar kotun taraiya dake Warri, jihar Delta.

Hukumar ta na zarginsa da wanda Kamilu wanda
zakara ya bashi sa’a ake nema ruwa a jallo a sakamakon aikata laifin almundahana na tsabar kudi naira 4,811, a yayin da suka zambaci wani dan
kasuwa mai suna Ebuwa Emmanuel Ikemefure.

Daga cikin zargin da ake yiwa wanda aka gabatar a kotun Tayo Morawo, sun karbi kudi hannun wani dan kasuwa tsakanin shekara ta 2016 zuwa
ta 2017 da jimlar su ya kama N4,811 bisa kulla huldar kasuwanci ta karya da suka yi da dan kasuwar.

Don haka kotu ta same su da aikata laifi wanda ya
saba sashe na 8 [a] zamba karbar kudin kafin alkalami na karya doka ta 2006 wanda Doka ta bayar da dama a hukunta wanda duk aka kama da aikata laifi irin wannan sashe na 1 [3]

Lauyan da yake kare wanda ake kara Tayo Morawo ya tsaya kaida fata cewa wanda ake zargin samsam bai aikata laifin da ake zargin sa da aikatawa ba yayin da lauyan da ya shigar da karar Moses Arumemi ya nemi kotu ta mayar da wanda ake zargi gidan kaso a ci gaba da tsare shi.

.Alkalin kotu mai shari’a Emmanuel Nwita ya daga sauraron shari’ar har sai nan da 18 ga watan da muke ciki domin lauyan wanda ake zargi barista Emmanuel Ajanana ya samu sukunin ci gaba da tattara bayanai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here