Masu Zamba Ta Yahoo Sun Addabi Jihar Delta

0
1069

Musa Muhammad Kutama Daga kalaba.

MATSALAR biyan kudin makaranta ya jefa wani yaro dan shekara 15 da haihuwa yin zamba ta kafar sada zumunta ko intanit da akafi sani da Yahoo a jihar Delta wanda lamarin ya yi kamari da ya addabi al’ummar jihar.

Yawanci ‘yan yahoo masu sana’ar zamba cikin aminci a jihar yara ne da aka kora daga makarantun boko kama daga makarantun sakandare zuwa jami’a saboda gaza biyan kudin makaranta.

Yanzu haka Al’ummar garin Abraka na jihar Delta na fama da wannan kazamar sana’a ta zamba cikin aminci wacce tayi kamari wanda har yara matasa sun mayar da sana’ar mai romo saboda kazamin kudin da suke samu ba dan kadan ba.

Wata majiya a garin Abraka ta tabbatar da cewa ‘yan yahoo yanzu har kananan yara suke horaswa a wannan bakar harka, su kuma manyan mazambatan na nan a jami’ar Abraka yadda idan sukayi amfani da karnukan farauta, su kan baiwa yara kashi arba’in cikin dari da aka samu.

Wani matashin dalibin makarantar sakandare mai suna Sunday da rana ta baci masa, ya shiga hannun ‘yan sanda kuma ya yi wa manema labarai Karin bayani akan yadda suke gudanar da al’amuran su.

Ya ce “na shiga wannan harka ta yahoo ne saboda iyaye na sun kasa ci gaba da biya min kudin makaranta suka ce basu da karfin kuma sai na ce ba matsala ni zan koyi sana’a da zan iya rike kaina har inci gaba da biyan kudin makarantar”.

Dalibin Sunday dan aji biyu a karamar sakandare ya ci gaba da cewa iyayen sa talakawa ne abinda wanda abinda za su ci ma gagarar su yake yi dan haka bayi da
wata madafa face ya fada wannan kazamar harkar.

A jihar Delta musamman yankin Abraka , yara matasa maza da mata sun rungmi harkar yahoo da gaske don ita ce kadai hanya da suke gani zata iya rabasu da talauci.

Hakazalika, ana zargin suna samun tallafin asiri na tsubbu daga malaman su na tsubbu da kan basu sa’a kamar yadda ake zargin wani daga cikin ‘yan tsubbun da laifin yiwa yaran saboda suna sallama mai kyau, shi ma kamin ya shiga hannu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan snadan jihar Delta ASP Chucks Orisewezie, ya tabbatarwa wakilin mu labarin inda ya ce “abin mamakin shi ne yara ne da wasun suke ‘yan jami’a, wasu kuma yan makarantun sakandire.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here