Duk Wanda Muka Gani Ba Katin Zabe Zamu Kama Shi

0
826
Mustapha Imrana Abdullahi Daga KADUNA.

KWAMISHINAN Yan sandan Jhar KADUNA Ahmad Abdurrahman ya bayyana gargadin cewa duk wanda suka kama ya na yawo ba tare da Katin Zabe ba, lallai za su kama shi kuma tsare shi a wuri mai kyau har sai an kammala zabe.

Kwamishinan Yan sandan ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da hukumar zaben mai zaman Kanta  ta shirya a kaduna kwana daya kafin gudanar da zaben na gobe asabar 9 ga watan nan.

“Abin da ake bukata a wurin mai jefa kuri’a shi ne Katin zabe, don hakan Idan muka samu wani ba tare da Katin Zabe ba zamu kama shi mu kuma ajiye shi a wuri mai kyau har sai an kammala zaben.

“Sai dai Kawai wadanda ke gudanar da aikin da ya sama muhimmi za a bari domin su gudanar da aikin su,kamar Yan jarida,ma’aikatan Lafiya,masu aikin kwana kwana da jami’an Yan sanda. Ko su Yan sandan Idan ba su da wata shaida ta cewa suna yin aikin zabe Na shekarar 2019 in an Gansu lallai za a kama su”, inji kwamishinan.

“Idan Muka ga wadanda wai suna ta yawo don Yan uwansu suna Takara Zamu kama su”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here