Hukumar  INEC Ta Raba Kayayyakin Zabe A Karamar Hukumar Lere

0
786
Isah Ahmed Daga Jos.

A YAYIN da hukumar zabe ta kasa INEC, ta bada tabbacin cewa ta kammala tura kayayyakin zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar a ranar asabar din nan, zuwa dukkan jihohin kasar nan.

Hukumar zaben ta INEC a Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna ta sami kayayyakin zabe kuma ta fara tura su zuwa dukkan mazabun karamar hukumar 11, don rabawa a rumfunan zabe guda 257 da ake da su a karamar hukumar, a yammacin wannan rana ta juma’a.

Da yake yiwa wakilinmu Karin bayanin kan shirye shiryen zabe baturen zabe na hukumar ta INEC a karamar hukumar  Alhaji Muhammad Iliyasu ya bayyana cewa sun sami dukkan kayayyakin zabe da ake bukata,  tun jiya alhamin.

Ya  ce yanzu suna aikin raba wadannan kayayyakin zabe ne zuwa mazabun wannan karamar hukuma 11. Daga nan kuma za a raba wadannan kayayyaki zuwa  dukkan  runfunan zabe da ke wannan karamar hukuma guda 457.

‘’Muna da ma’aikata 1800 da zasu yi aiki a wadannan rumfunan zabe. Muna sa ran gobe kafin karfe 8 na safe, kowanne ma’aikaci yana rumfar zaben da aka tura shi. Don haka muna kira ga jama’a su daure su fito, domin a zaben da ya gabata  mutane basu fito ba, kamar yadda ya kamata. Don haka muna kira ga jama’a su daure su fito a wannan karo’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here