Jam’iyyu 25 Sun Shiga Jirgin Murus A KADUNA

  0
  1302
  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna.
  GAMAYYAR kungiyar jam’iyyu masu ragista Sun yanke shawarar marawa Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i baya domin ya lashe zaben ranar Asabar Mai zuwa.
  Shugabannin Jiha Na wadannan jam’iyyu Ashirin da biyar karkashin kungiyar jam’iyyu masu ragista suka bayyana wa manema labarai hakan a Kaduna.
  Da suke karanta takardar da ke dauke da sa hannun shugaban kwamitin amintattun da sakataren kungiyar Saddiq Mai Lafiya da kuma Ambasada Shehu Mai Lafiya Makaman Gado da Masun Zazzau duk Sun tabbatar da cewa Sun yanke wannan hukunci ne saboda basa son ci gaba da bayar da goyon baya ga PDP da suka Ce ita ta jefa kasar nan cikin halin da take ciki a halin yanzu.
  “Duba da irin yadda Gwamnan Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ke tafiyar da shugabanci a Jihar da ya kawo ci gaba a fannonin Lafiya,Ilimi da samar da tituna, hakan yasa suka yanke hukuncin ci gaba da Bashir goyon baya domin ya kammala ayyukan da yasa a gaba”. Inji su.
  Kuma Gwamnan Kaduna ne ya bayar da cikakkiyar dama ga daukacin kananan hukumomi 23 inda ake ba su kudinsu mai tsaye ba tare da kowa ya cire masu komai ba da bashi a tsarin doka.
  Da wannan ne muke ganin ya dace tun da wuri mu ci gaba da kokarin taimakawa yayanmu da Jikoki ta yadda za su sani makoma Mai kyau a nan gaba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here