An Bindige Dan Majalisar Wakilan Tarayya Har Lahira

0
695

Daga Usman Nasidi.

DAN majaisar wakilan tarayaa mai wakiltan mazabar Lagelu/Akinyele a jihar Oyo, Hanarabul Temitope Olatoye Sugar, ya rasa rayuwarsa da yammacin nan.

Mun samu rahoton cewa an garzaya dashi asibitin jami’ar Ibadan bayan wasu yan baranda sun bindigeshi a birnin jihar.

Kakakin asibitin jami’ar Ibadan UCH, Toye Akinrilola, ya tabbatar da cewa an kawo dan majalisan asibitin cikin mumunan hali bayan an harbesa a fuska.

Likitocin da ke cikin sashen jinyar gaggawa sunyi iyakan kokarinsu wajen cecen rayuwarsa amma ya kwanta dama. Ya mutu yana mai shekaru 47.

Hakazalika, mun samu rahoton cewa akalla mutane uku sun rasa rayukansu da safiyar ranar zabe a jihar RIvers, kuku maso kudancin Najeriya.

Wani matashi mai sune Micheal Abednego, ya gamu da ajalinsa ne a hannun wani jami’in dan sanda a karamar hukumar Ahaoda ta yamma dake jihar.

Hakazalika, wata jigor jam’iyyar APC da a’a gano sunanta ba har yanzu da wani matashi suna rasa rayukansu a karamar hukumar Ndoni, Ogba/Egbema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here