A HALIN yanzu, ana ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna da na yan majalisar dokokin jihar kano tun bayan gudanar da zaben jiya asabar kamar yadda akayi a fadin kasarnan.
Wakilin mu ya ruwaito cewa tun a daren jiya ne wasu wadanda basu da wata alaka da hukumar zabe suke bayyana sakamako iri daban-daban wanda dole sai da hukumar zabe mai zaman kanta a jihar ta kano ta bada sanarwar cewa ita ce kadai ta ke da alhakin bayyana sakamakon zabe bisa doka, tare da gargadin al’uma kan bayyana sakamako batare da fitar daga hukumar zaben ba.
Haka kuma a daren na jiya har wasu abokan hamayya sun fara gangamin murnar lashe zabe sakamakon yadda wasu suka rika bayyana sakamakon zabe marar inganci lamarin da ya sa su Kansu hukumomin tsaro suka rika gargadin fitowa kan tituna domin murnar cin zabe.
Ya zuwa aiko da wannan labari, jami’an hukumar zabe mai zaman kanta watau INEC na yankunan kananan hukumomi suna ci gaba da kai sakamakon zabukan gwamna da na yan majalisun dokokin da aka gudanar jiya asabar, wanda a cewar hukumar zaben, sakamakon da ya fita daga gare ta shi ne sahihin sakamako ba wanda kawai wasu suke kirkira ba.

Mata a Layin zabe a rumfar zabe ta Zangon Mata dake Mazabar Ganduje.