PDP Ta Lashe Akwatin Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna A Zaben Gwamna

  0
  1039

  Usman Nasidi Daga Kaduna.

  RAHOTANNI daga gwamnatin Jihar Kaduna na bayyana cewa mai girma gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufai na jihar ya gaza kawo akwatin da ke cikin rumfar gidan Gwamnatin Jihar Kaduna inda yake mulki a halin yanzu.

  Jam’iyyar APC mai mulki ta sha kayi ne a hannun PDP mai adawa a cikin fadar Sir Kashim Ibrahim da ke Garin Kaduna. Isa Ashiru ne PDP ya samu kuri’u 145, yayin da El-Rufai ya samu kuri’a a 114 a rumfar fadar.

  Sai dai ba mu sa labari game da zaben ‘yan majalisar dokoki a akwatin na PU 013 da ke cikin fadar gwamnatin jihar Kaduna ba. A akwati na biyu (watau PU 014) da ke cikin fadar, PDP ta samu 109 yayin da APC ke da kuri’a 84.

  A mazabar gwamnan kuma inda yake kada kuri’a, APC ta samu kuri’u 367. Nasir El-Rufai yayi wa babban abokin hamayyar sa watau Isa Ashiru ne PDP wanda ya samu kuri’a 59 mugun bugu ne a rumfar Unguwar Sarki.

  Abdullahi Sadiq shi ne jami’in hukumar zabe mai zaman kan-ta na kasa watau INEC da ya sanar da sakamakon zaben na akwatin farko na cikin Unguwar Sarki da ke cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa a jihar Kaduna.

  Tuni dai gwamnan ya kada kuri’ar sa ya kuma koma bakin aiki a ofishin sa duk da ana hutu. Rt. Hon. Isa Ashiru Kudan shi ne wanda yake karawa da gwamna Nasir El-Rufai’s a zaben na bana.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here