Yan Bindiga Sun Kone Gidaje A Unguwar Barde Kaduna

0
956

Usman Nasidi Daga Kaduna.

RAHOTANNI na bayyana cewa wasu yan bindiga na nan suna kone-konen gidaje a kauyen Angwan Barde, karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna.

Wani jigon garin da ya nemi a boye sunansa ya fada ma manema labarai cewa maharan na a hanyarsu na komawa wani garin da ke kusa bayan sun kai farmaki Angwan Barde.

Yakubu Sabo, Kakakin yan sandan jihar Kaduna, bai amsa kiran wayarsa ba inda aka aika masa sakon waya kan lamarin.

Harin farko da aka fara kaiwa Angwan Barde ya kasance a ranar Juma’a, 11 ga watan Fabrairu, lokacin da wasu da ake zargin makaiyaya ne suka kai farmaki kauyen da tsakar dare sannan suka kashe mutane 11.

Harin na zuwa ne kasa da kwanki 12 bayan an kashe mutane 40 da kuma kona gidaje da dama a kayen Karamai, duk a karamar hukumar Kajuru da ke jihar.

Yace kashe-kashen ya fara ne inda aka kai wa wasu manoma a yankin hari a ranar Asabar.

Harin ya yi sanadiyar wasu hare-haren ramuwar gayya sannan mutane da dama sun mutu. Gwamna Nasi El-Rufai ya bayyana adadin wadanda suka mutu a matsayi 130.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi Allahwadai da sabon harin da aka kai kuma ta bukaci a al’ummar yankin da su kwantar da hankalin su ayayin da aka tura jami’an tsaro don kara tabbatar da tsaro a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here