El-Rufa’i Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kaduna

0
1100

Usman Nasidi Daga Kaduna

BAYAN kammala tattara alkaluman sakamakon zaben gwaman jihar Kaduna wanda hukumar zabe mai zaman kan ta watau INEC ta gudanar a ranar asabar 9 ga waran Maris, an bayyan Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Malam Nasiru El-Rufa’i a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben.

Da yake jawabi bayan kammala tattara sakamakon zaben, Farfesa Muhammad yahuza Bello a madadin hukumar INEC ta kasa, ya bayyana malam Nasiru El-Rufa’i na jam’iyyar APC ne wanda ya yi nasarar lashe zaben da kuri’a 1,045,427, yayin da Ashiru Kudan na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 814,168.

Jahar Kaduna na daya daga cikin jihohin da gwamnanta, Nasir El-Rufai ya nemi zarcewa don yin dare dare akan karagar mulki, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Isah Ashiru Kudan ya kalubalanceshi a takarar.

Amma daga karshe bayan tattara alkalumman sakamakon zaben daga kananan hukumomin jahar guda 23 gaba daya, gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai ne ya samu gagarumar nasara da bambamcin kuri’u 231, 173 inda yayi ma Isah Ashiru da jam’iyyar PDP murus kamar yadda yake cewa.

Ga dai yadda sakamakon suka kasance:
1, Kubau
APC – 57,182
PDP – 17,074

2, Ikara
APC – 41,969
PDP – 22,553

3, Kudan
APC – 28,624
PDP – 22,022

4, Kaura
APC – 8,342
PDP – 38,764.

5, Makarfi
APC – 34,956
PDP – 22,301

6, Jaba
APC: 6,298.
PDP: 22,976

7, Kajuru
APC – 10,229
PDP – 34,658

8, Giwa
APC – 51,455
PDP – 19,834

9, Kauru
APC -34,844
PDP – 31,928

10, Kachia
APC – 30,812
PDP – 51,780

11, Soba
APC – 55,046
PDP – 25,440

12, Zangon Kataf
APC – 13,448
PDP – 87,546

13, Sanga
APC – 20,806
PDP – 21,226

14, Kaduna ta Arewa
APC – 97,243
PDP – 27,665

15, Birnin Gwari
APC – 32,292
PDP – 16,901

16, Chikun
APC – 24,266
PDP – 86,261

17, Sabon Gari
APC – 57,655
PDP – 25,518

18, Lere
APC – 71,056
PDP – 45,215

19, Jema’a
APC – 21,265
PDP – 63,129

20, Kagarko
APC – 21,982
PDP – 26,129

21- Zaria
APC : 111,014
PDP: 35,356

22- Igabi
APC: 102,612
PDP: 31,429

23- Kaduna ta kudu
APC: 102,035
PDP: 37,948

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here