Har Yanzu Ana Dakon Cikon Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kano

0
1242

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

KAMAR yadda rahotanni suke  tafiya,  batun sakamakon zaben gwamna a jihar kano yana tafiya kusan kafada-kafada tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje  na jam’iyyar APC da babban mai kalubalantar sa  Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP bisa yadda hukumar zabe mai zaman kanta take bayyanawa.

Sai dai har  ya zuwa aiko da wannan rahoto watau karfe  1:43, gwamna Ganduje  na jam’iyyar APC shine a kan gaba da kuri’a dubu 852,157 yayin da  Abba Kabir yake  da dubu 806324 kamar  yadda ita hukumar zaben ta bayyana, sannan gwamna Ganduje yana da jimlar kananan hukumomi 24 cikin kananan hukumomi talatin da aka sami sakamakon zaben su.

Ya zuwa yanzu dai, al’umar jihar kano suna dakon  sauran sakamakon zabukan tareda ganin an bayyana wanda  ya lashe wannan zabe ganin yadda kano take da muhimmanci a siyasar kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here