Yadda Zabe A Garin Maiduguri Da Damaturu Ya Gudana

0
1146

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

ZABEN gwamnoni da na ‘yan majalisun Jihohi da aka gudanar a fadin kasar nan a ranar asabar 9 ga watan nan na Maris 2019, an samu karancin fitowar jama’a masu kada kuri’a a jihohin Borno da Yobe, a binciken da wakilinmu ya gudanar a wasu rumfunan zabe a Maiduguri da Damaturu, musamman idan an kwatanta da zaben shugaban kasa da ya gabata a makonni biyu da suka shude.

A tattaunawar da wakilin mu ya yi da wasu masu jefa kuri’a, a wasu rumfunan zabe a wasu unguwannin Damaturu kamar pomfamari, kofar mai martaba Sarkin Damaturu da kuma ta wayar tafi da gidanka a wasu unguwannin birnin Maiduguri da suka hada da Baga Road, Gwange, Bolori da Bulumkutu, sun bayar da tabbacin hakan tare da bayyana dalilai mabambanta dangane da karancin fitar jama’a zuwa zaben.

A rumfar dake kofar mai martaba Sarkin Damaturu wata jami’ar hukumar INEC; Hafsat Sale Umar ta bayyanawa wakilin namu kan cewar tun wajen kimanin karfe 7:00am na safe, suke zaune amma mutane kadan suka tarar, kuma kamar yadda aka gani, babu jama’a sosai duk da bata san dalilin da ya hana jama’a yin tururuwar fitowa ba kamar yadda aka yi a zaben baya.

Ta ci gaba da cewar su dai a bangarensu, babu wata matsalar da suke fuskanta ko kadan musamman dangane da kayayyakin zabe.

Shi kuwa Abdullahi Musa a mazabar unguwar Bulumkutu, da ke garin Maiduguri, ya bayyanawa wakilinmu ta wayar tafi da gidanka cewar, “mafi yawan masu zabe sun fi damuwa da zaben shugaban kasa- ta dalilin Buhari kawai saboda Buhari ya kayar da Atiku, da kuma yadda da taimakon Allah ya yi hobbasan samar da zaman lafiya a yankin.

Haka nan Abdu Shuwa, wanda ya jefa kuri’ar sa a mazabar Baga Road a birnin Maiduguri ta wayar tafi da gidanka ya ce, “ni a nawa tunani shi ne an samu karancin fitar jama’a ne; sabanin na shugaban kasa, a jihar Borno, a zaben gwamnoni shi ne saboda yadda kowa ya sani kan cewa aikin gama ya gama, don haka wa kake ganin zai iya karawa da Farfesa Zulum (APC)?”

Yayin da shi kuma Malam Sabo Isa, dan gudun hijira a sansanin Mogolis ya bayyana cewa, “ta ya ya ba za a fuskanci karancin fitar masu jefa kuri’a ba, alhalin kusan duk manyan PDP sun riga sun kaura zuwa APC a ‘yan kwanaki kafin zaben? Wanda kusan duk ‘yan takarar PDPn da ake sa ran a zaba duk suma sun sallamar, to wa za a zaba?”

Da wakilinmu ke tambayar kwamishinan hukumar INEC a jihar Yobe, Alhaji
Ahmad Makama, kan karancin jama’a a lokacin da yake rangadin gani da
ido kan yadda zaben ke
gudana, ya bayyana kan cewa, ba za a yi gaggawar yanke hukunci kan yanayin karancin fitowar masu jefa kuri’ar ba- ganin cewa
ai da sauran lokaci.

Alhaji Makama ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, bai wuce awa
guda da fara gudanar da zaben ba, ba za iya yanke hukunci kan karancin
fitowar jama’a ba ko a’a. Amma dai ko ba komai, mu abinda ya dame mu shi ne, zaben zai ci gaba da gudana har zuwa karfe 2:00 na yamma lokacin da za a ja layi.

Kwamishinnan zaben ya kuma nuna gamsuwar sa dangane da yadda zaben ke
gudana, a cikin tsari da tsanaki, tare da cewa, babu wani korafin tangarda da muka samu, kuma zaben yana gudana a cikin tsari a dukan rahotanin da ma’aikatan mu suka aiko mana a fadin jihar Yobe”.

A hannu guda kuma wani wakilin jam’iyyar PDP (agent) a wata rumfar
zabe a garin Damaturu, ya shi ma ya bayyana gamsuwar sa dangane da
yadda zaben ya gudana a cikin tsanaki, babu wata hatsaniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here