Matasan APC Sun Yi Zanga-Zangar Lumana A Fatakwal

0
818

Musa Muhammad Kutama Daga kalaba.

DARURUWAN Magoya bayan jamiyyar APC ne suka fantsama kan manyan titunan garin fatakwal hedkwatar jihar riba suna wake-waken jamiyyar dauke da kwalaye domin nuna takaicin su akan matakin da hukumar zabe mai zaman kanta da dauka na dakatar da zabe a jihar ribas.

Magoya bayan jamiyyar sun bi kan babbar hanyar unguwar gidajen gwamnati wato GRA suka bi ta kan babbar hanyar Aba wadda ta nufi jihar Abiya wacce ta ke hanya mafi girma ta shiga da fita garin fatakwal.

Su dai magoya bayan jamiyyar suna nuna bakin cikin su ne game da dakatar da zabukan gwamna dana majalisar dokoki Jiha da hukumar INEC ta yi.

Haka nan kuma magoya bayan APC sun yi kiran da a kama babban baturen zaben jihar ribas Obo Effanga, bisa zarginsa da taimakawa wajen yin magudin zabe da kuma kin baiyana sakamakon zaben kamar yadda ya kamata.

A jawabinda ya yiwa masu zanga-zangar lumanar, shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa-da kasa Dokta Omenazu Jackson Chancellor ya ce kin sanar da sakamakon zaben tsabagen son zuciya ne na baturen zaben wanda ya saba dokar zabe ta kasa.

Daga nan ya bukaci shugaban hukumar zabe ta kasa Mahmood Yakubu ya sanya baki akan na jihar ribas don a gaggauta sanar da sakamakon zaben gwamnan dana ‘yan majalisun jihar da aka yi domin samun zaman lafiya da kaucewa fadawa rikici.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here