Sarkin Kano Ya Jinjinawa Kwamishinan ‘Yan Sanda CP Wakili

0
1067

Daga Usman Nasidi

MAI Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na ll ya yi godiya ta musamman ga Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Kano, CP Mohammed Wakili da sauran jami’an tsaro kan irin rawar da suka taka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar yayi takaddamar zaben gwamna da ya gabata.

Wannan jinjina da yabon dai na zuwa ne a cikin wata fita da manema labarai da sairkin yayi a fadar sa bayan da aka gudanar da zaben gwamnoni da kuma ‘yan majalisar jiha a fadin kasar a ranar 9 ga watan Maris.

Sarkin ya bayyana cewa hukumar INEC ce kadai ke da ‘yancin bayyana sahihin sakamakon zabe, inda hukumar ta bayyana cewa zaben bai kammala ba, kuma akwai wasu mazabu da za a sake zabe a jihar.

Daga nan, sarkin sai ya yi kira ga al’ummar Kano da su zauna lafiya kuma su kwantar da hankali da kuma kiyaya yada jita jita.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jami’an ‘yan sandan na jihar Kano karkashin jagorancin shugaban na su sun kama mataimakin gwamnan jihar da kwamishin kananan hukumomi da ma shugaban karamar hukumar hukumar Nasarawa da laifin kokarin yin magudi.

Wannan dai ya ja ma ‘yan sandan farin jini sosai inda ake cigaba da yaba masau musamman ma ganin yadda ba kasafai ake kama masu rike da mukamai ba da laifi a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here