Shugaba Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Harin Jihar Kaduna

0
1140

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da mumunan harin da aka kai a karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna.

Buhari ya ce babu wani shugaba da zai kwanta barci hankalinsa kwance alhalin talakawansa na fama da matsalar hare-haren ta’addanci.

An rahoto cewa akalla mutane goma ne aka kashe a wannan hari.

Shugaban kasar yace: “Irin wadannan mutane da ke aikata irin wannan ta’asa ba su da tunanin mutane a zuciyar su.

“Duk da cewa gwamnati tana iya bakin kokarin ganin ta kawo karshen wannan abin tashin hankali dole ne sai suma mutane sun hada kai da gwamnati wajen gani an kawo karshen haka.

Buhari ya koka da yadda aka maida komai siyasa a kasarnan har da rayujan mutane ba a dauke shi da daraja ba “Da zarar za ana kokarin bankado irin wadannan mutane masu zuga matasa sai ayi wa gwamnati caaa, cewa wai ba za a tuhumi na su ba.

“Kiyayya da mutane suka saka zukatan su ga juna shine babban dalilin da ya sa ba a iya gano farko ballantana yadda za a iya kawo karshen wannan matsala.”

Baya ga wannan hari da aka kai a Karamar hukumar Sanga, Karamar hukumar Kajuru ma suna fama da irin wadannan hare-hare domin a ‘yan kwanakin nan ma sai da aka rika kai hari kauyukan karamar hukumar Kajuru.

Baya ga irin wadannan hare-hare, kauyuka Birnin Gwari ma na fama da ayyukan mahara da masu garkuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here