‘Yan bindiga Sun Kai Hari Filato: Sun kashe Shanu 81, sun sace 32

0
1106

Daga Usman Nasidi.

SHUGABANNIN kungiyar makiyaya ‘Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da ‘Fulani Youth Association of Nigeria (FYAN)’ a jihar Filato, sun yi zargin cewar wasu ‘yan bindiga sun kashe shanu 81 tare da sace wasu 32 a wani hari da suka kai kusa da wata makaranta a Kwall dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

MACBAN da FYAN sun bayyana cewar babu wani dalilin da yasa za a kai harin a kan mutanensu.

Shugaban kungiyar MACBAN a jihar Filato Muhammad Nura Abdullahi, ya shaidawa manema labarai cewar ‘yan bindigar sun harbe shanu 81 yayin da suka kashe wasu ta hanyar caccaka masu adda.

Sannan ya kara da cewa sun sace shanu 32 tare da raunata 48 da aka garzaya da su zuwa kwata don gudun sake yin asarar su.

Abdullahi ya kara da cewa sun sanar da rundunar soji ta ‘operation safe haven (OPSH)’ da kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Isaac Akinmoyede, a kan harin kuma sun turo wakilai domin daukan kididdigar barnar da ‘yan bindigar suka tafka.

“ Rundunar sojin OPSH ta san da maganar kai harin sannan na sanar da kwamishinan ‘yan sanda da kai na wanda a bisa shawarar sa ne na sanar da DPO na yankin. Kwamanda da DPO sun ziyarci wurin da ‘yan bindigar suka kai harin, ” a cewar Abdullahi.

Shi kuwa Saeedu Maikano na FYAN cewa ya yi an kai harin ne da gan-gan domin tunzura makiyayan tare da bayyana mamakinsa a kan yadda har yanzu gwamnatin jihar Filato ba ta fitar da jawabin Alla-wadai da kai harin ba.

A cewar Maikano; “ yanzu gwamnati na nufin Kenan ba zata iya kare mu da dukiyoyin mu ba? Shin sun san tsawon lokacin da ake dauka kafin a raini Saniya daya har ta girma? Da gan-gan aka kai wannan harin kuma babu wata niyya a wurin gwamnati na ba mu kariya.”

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Filato Tyopev Terna, ya ki yarda ya ce komai a kan harin duk da manema labarai sun nemi ya yi Karin bayani a kan hakan.

Manjo Adam Umar na OPSH ya tabbatar da kai harin tare da bayyana cewar ‘yan bindigar sun kada shanun zuwa daji kafin daga bisani su harbe su.

Sai dai ya ce ba zai tabbatar da adadin shanun da aka kashe ko aka sace ba don a halin yanzu suna kokarin gano su waye wadanda su ka kai harin, kuma tuni an bi sahun su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here