Matasan Dake Tattakin Zuwa Jihar Kano, Sun Kara Mikar Hanya Daga Zariya

0
1104

Usman Nasidi Daga Kaduna.

A CI gaba da kokarin da suke na ganin cewa hakarsu ta cimma ruwa akan nuna goyon bayansu ga Dan takarar gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP, matasan dake tattakin zuwa Jihar Kano daga garin Kaduna sun Isa garin Zariya kamin su sake mikar hanya.

Matasan Nazifi Abbas da Mohammed Auwal Abdullahi sun isa garin Zariya ne yau litinin da misalin karfe biyun rana inda suka dan huta ayayin da suka kai ziyara ofishin kwankwasiya dake cikin garin inda suka gana da sauran yan uwansu bayan sun baro garin Kaduna a jiya da safe.

A zantawarsu da wakilinmu ta waya, matasan yan kasa da shekaru talatin, sun bayyana cewa sun kwana a garin Yalwa ne inda sarkin Garin ya yi musu masauki kamin su sake mikar hanya da wayewar gari inda suka isa garin Zariya da suka ziyarci yan uwansu na kwankwasiya suka amshe su a ofishin su dake garin.

Nazifi Da Auwal Tare Da Sarkin Yalwa

 

Sun ce, a halin yanzu sun tasan ma garin Makarfi a yayin da suka baro lukoro, duk da yake suna jin idan sun ga da hali zasu iya kara nausawa gaba inda zasu nemi waje don yada zango kamin idan Allah Ya nufe mu da kaiwa gode da rai da lfy sai su dora daga inda suka tsaya.

Acewarsu, a halin yanzu babu wata matsala ko turjiya da suke fuskanta a hanyarsu ta tafiya, kana kowannen su na cikin kashin lafiya sai dai suna kara bukatar yan uwa da abokan arziki da su ci gaba da taya su addu’a na ganin cewa sun cimma burin nasu na yin tattakin har zuwa garin kano inda suka saran yan uwansu na kwankwasiya dake chan zasu tarbesu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here