Abubuwan Da El-Rufa’i ke Yi A Kaduna Abubuwa Ne Da Zasu Kawo Ci Gaba – Ramin Kura

0
1240

Isah Ahmed Daga Jos.

TSOHON shugaban Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna kuma tsohon sakataren Hukumar agajin gaggawa ta Jihar Kaduna Alhaji Aliyu Sale Ramin Kura ya bayyana cewa abubuwan da gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’I yake yi a Jihar, abubuwa ne da zasu kawo cigaba. Alhaji Aliyu Sale Ramin Kura ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Alhaji Aliyu Sale wanda ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar APC bayan zaben shugaban shugaban kasa, ya ce abubuwan da gwamna Nasiru yake yi a jihar Kaduna abubuwa ne da zasu kawo cigaba.

Don haka ya shawarci masu kawo rikice rikice a jihar, su yiwa Allah su bari domin a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Ya ce da su aka kafa jam’iyyar PDP kuma tun lokacin da aka kafa ta, bai taba fita daga wannan jam’iyya ba, sai a wannan lokaci.

‘’Babban abin da yasa na fita daga cikin jam’iyya PDP na koma jam’iyyar APC shi ne ni mai ra’ayin a cigaba ne. Kuma na lura gwamnatin shugaba Buhari da gwamnatin Nasiru El-Rufa’i masu son cigaba ne’’.

Alhaji Aliyu Sale ya yi bayanin cewa misali aikin ruwan Zariya da gwamnatin EL-Rufa’i take yi tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ne ya kirkiro shi, lokacin da yake gwamnan Jihar.

Ya ce wasu gwamnonin PDP sun zo, amma basu cigaba da wannan aiki ba. Amma Malam Nasiru ya cigaba da wannan aiki.

Ya ce shi babbar damuwarsa ta ita ce abin da ya shafi cigaban al’ummar Najeriya. Wannan shi ne yasa ya fita daga PDP ya dawo APC, domin ya bada tashi gudunmawar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here