KO SAU 10 ZA A YI ZABE A KANO ABBA GIDA GIDA NE ZAI LASHE – NAFI’U JOS 

  0
  1404

  Isah Ahmed Daga  Jos

  TSOHON shugaban Kungiyar matasa ta yakin neman zaben shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP  na Alhaji Sule Lamido na shiyar jihohin arewa ta tsakiya, Alhaji Nafi’u Ya’u Jos ya bayyana cewa ko sau 10 za ayi zaben gwamna a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP ne zai lashe zaben.

  Alhaji Nafi’u Ya’u Jos ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos, kan yadda aka gudanar da zaben gwamnan Jihar Kano.

  Ya ce a wannan zabe da ya gabata an so a nunawa jama’iyyar PDP karfin gwamnati a jihar Kano domin kowa ya sani cewa Abba Gida Gida na jam’iyyar PDP ne ya lashe wannan zabe na kujerar gwamnan Jihar Kano.

  Ya ce ba a jihar Kano ne kadai aka yi zaben gwamna ba. An yi zaben  a Jihar Kwara amma da yake APC ce ke kan mulki ta ci zabenta, kuma gwamnan da yake kan mulki na jam’iyyar PDP da Sanata Bukola da ya fadi suka  taya gwamnan APC da ya ci zaben murna.

  ‘’ Yadda wannan zave ya nuna Abba Gida Gida ne ya cinye dukkan  kananan hukumomin Jihar Kano  44,  don haka  muna jira ne a karasa zaven  a ranar asabar din nan, a sanar cewa shi ne ya lashe wannan zabe’’.

  Ya yi  kira  ga hukumar zabe ta INEC  tayi  ingantatcen zabe   wanda kowa zai yarda da shi a wannan kammala zabe da za a gudanar a Jihar Kano.

  Har’ila yau ya yi  kira ga magoya bayan jam’iyyar PDP na jihar Kano su kwantar da hankalinsu, su fito su jefa kuru’unsu su koma gidajensu in Allah ya yarda zasu ci wannan zabe.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here