JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
MATASAN nan guda biyu da suka tashi daga Kaduna zuwa kano a kafa watau Nazifi Abbas da Muhammad Auwal Abdullahi sun isa birnin kano da misalin karfe uku na yammacin wannan rana ta Laraba kamar yadda suka yi alwashi.
Da suke zantawa da wakilin mu na jihar Kano, Nazifi Abbas da Auwal Abdullahi sun bayyana cewa sun kuduri aniyar yin wannan tattaki ne domin nuna cikakken goyon bayan su ga dan takarar gwamnan jihar ta kano a tutar jam’iyyar PDP, watau Injiniya Abba Kabir Yusuf da kuma jagoran kwankwasiyya na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kuma dimokuradiyya.
Matasan sun kara da cewa tun da suka bar Kaduna babu wata matsala da ta faru garesu, sannan sun yi tattaki cikin lumana da farin ciki matuka bisa yadda al’uma suka rika tsayawa wajensu suna jinjina masu tareda tallafa masu da abinci da ruwan sha da sauran dawainiya irin ta kauna.
Bugu da kari, matasan sun sanar da cewa sun isa kano ne domin su bada tasu gudummawar ga jam’iyyar PDP domin ganin dan takarar ta Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sami nasara a zaben da za’a kammala ranar asabar mai zuwa idan Allah ya kai mu.
Ya zuwa aiko da wannan labari, dumbin matasa ne suke yin rakiya ga wadannan matasa masu tattaki daga Kaduna zuwa Kano Inda ake ta jinjina masu da nuna goyon bayan abin da suka yi.