Na Rungumi Kaddarar Faduwar Zaben Gwamna Da Na Yi—Dan Takarar SDP

  0
  704

  Musa Muhammad Kutama, Daga kalaba

  DANTAKARAR mukamin gwamna a zaben tara ga watan maris a karkashin jam’iyyar SDP a jihar kuros riba Eyo O. Ekpo, ya ce ya rungumi kaddara faduwar zabe da ya yi na takarar neman mukamin gwamnan jihar kuros riba da ya yi a zaben da akayi makon jiya

  Hakan na zuwa ne bayan da hadakar gwamnonin sauran jam’iyyu da suka yi takarar mukami daya da gwamnan mai ci yanzu wanda ke wa’adi na biyu karkashin jam’iyyar PDP ya yi nasarar lashen zabe da aka yi yasa suka yi mubayi’a ga gwamnan domin yaci gaba da aiyukan ciyar da jihar gaba da ya fara shekaru hudu da suka gabata hawan sa na farko.

  Ya ce “ Na rungumi kadddara faduwar zabe da nayi a takarar gwamnan jihar kuros riba dana fito nasan mulki Allah ke bayar dashi ga wanda yaso shi kuma ke hanawa wanda yaso don haka ni na yarda da hukuncin da Allah ya zartar akaina na yadda nasha kasa a zaben da aka yi kamar yadda Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP Donald Duke yasha kasa.

  A zantawarsa da Wakilin mu, Eyo Ekpo dan takarar gwamnan jam’iyyar SDP a kuros riba, ya bayyana cewa bazai taba mayar da kansa saniyar tatsa ba a wurin lauyoyi don haka ya gwammace ya taya gwamnan wanda ya yi nasara kan zaben yake wa’adi na biyu da addu’a domin ya samu cin nasarar gudanar da aikinsa kamar yadda ya fara shekara hudu da suka gabata.

  Ya ci gaba da cewa irin yadda gwamna Ayade ya dauko aiyukan ci gaban raya kuros riba kamata ya yi su taya shi da addu’a ba su runtuma zuwa kotu ba.

  A wata sanarwar da shugaban gamayyar jam’iyyu ta Najeriya wato CNPP na kuros riba Micheal Sunday ya fadi a ganawar da sukayi da manema labarai a ofishin jam’iyyar ya bayyana cewa “daukacin wadanda suka yi takarar mukamin gwamnan jihar kuros riba a inuwar jam’iyyu daban-daban a jihar su goma sha biyu ne suka hadu suka ce sunyi mubaya’a ga wanda ya lashe zaben wato gwamnan jihar kuros riba farfesa Ben Ayade.

  shugaban wanda ya yi Magana a madadadin daukacin wadancan ‘yan takara da suka yi takara ya ce sun yanke shawarar ce da nufin amarawa gwamnan baya ya samu nasara kan aiyukan raya jihar da ya fara.

  Ya ce “shekara hudu tayi kadan a aikin raya jiha da gwamnan ya yi gashi kuma bai gama ba don haka akwai bukatar a sake bashi wata damar ya karasa aiyukan raya jiha da ya fara tun farko.”

  ‘Yan takarar haka nan kuma sunyi Allah wadai da kin kiran gwamna Ayade su tayashi murna da ‘yan takarar mukamin a karkashin jam’iyyun APC da SDP suka yi.

  A cewar su wannan rashin kiran gwamnan su taya shi murnar nasarar da ya yi akan su a zaben daya gudana, bashi da wani amfani.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here