Kungiyar Masu Shayi Ta Bukaci Buhari Ya Dubi Matsalar Farashin Kayan Masarufi

0
1036

Isah Ahmed Daga Jos.

KUNGIYAR masu shayi ta Najeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya dubi matsalar tashin farashin kayayyakin shayi da sauran kayayyakin masarufi da ake fama da shi a kasar nan.

Shugaban kungiyar na Najeriya Alhaji Sha’aibu Abubakar ne ya bayyana bukatar kungiyar, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.

Ya ce al’ummar Najeriya musamman talakawa sun amince cewa shugaba Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, don haka suka jajirce kan dole sai ya koma kan kujerar shugabancin kasar nan, kuma gashi Allah ya bashi nasara.

‘’Don haka muna fatar shugaba Buhari zai dubi al’ummar kasar nan, musamman wajen gudanar da ayyukan raya kasa kamar bunkasa bangaren ilmi da kiwon lafiya da hanyoyin mota da kuma duba matsalar tashin farashin kayayyakin masarufi, domin a sami rage radadin talaucin da ake fama da shi a kasar nan’’.

Har’ila yau ya yi kira ga shugaban kasar kan ya tallafawa wannan kungiya da sauran qungiyoyin da suke gudanar da sana’o’i a kasar nan.

Ya ce gaskiya a karon farko na gwamnatin Buhari sun yi ta kai kokensu har ya zuwa Abuja amma basu sami nasarar share masu hawaye ba. Don haka ya yi fatar a wannan karon, za a tausaya masu a share masu hawaye musamman wajen magance masu matsalar tashin farashin kayayyakin da suke gudanar da wannan sana’a.

Daga nan ya yabawa al’ummar Najeriya kan yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya da gwamnonin jihohi da ‘yan majalisun jihohi lafiya.

Ya ce babu shakka wannan babban abin farin ciki ne ga dukkan al’ummar Najeriya kan yadda aka gudanar da wadannan zabubbuka lafiya. Ya ce wannan ya nuna cewa damakoradiya ta fara zama da gindinta a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here