HUKUMAR zabe mai zaman kanta watau INEC ta bayyana gwamna Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar kano da aka kammala jiya asabar sakamakon sake jaddada zabe da aka yi a wasu kananan hukumomi 28.
Da yake bayyana sakamakon zaben, jami’in tattara sakamakon zabe na hukumar, farfesa Bello Shehu ya ce an sanar da wanda ya ci wannan zabe ne ta hanyar kammala sakamakon zaben da aka gudanar asabar din data gabata kamar yadda tsarin hukumar zabe yake.
Farfesa Bello ya ce gwamna Ganduje na jam’iyyar APC ya sami kuri’u 1,033,695 yayin da Abba Kabir na jam’iyyar PDP ya sami 1,24,713 wanda hakan ta sanya gwamna Ganduje ya bashi tazarar kuri’u 8,982.
Tuni dai magoya bayan jam’iyyar ta APC suka ci gaba da gudanar da bukukuwan murnar samun nasara tareda yiwa gwamna Ganduje fatan Allah ya taya riko kamar yadda al’adar zabe take.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa taimakawar shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole yayin da ya daga hannun gwamna Ganduje a matsayin dan takarar gwamnan kano a tutar APC.