Kotu Ta Daga Sauraron Karar El-Zakzaky Har Sai Baba-Ta-Gani

0
722

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WATA babbar kotun jihar Kaduna karkashin mai shari’a Gideon Kurada ta daga sauraron karar da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da shugaban kungiyar mabiya shi’a (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, har sai baba-ta-gani.

Alkalin kotun ya bayyana cewar ya daga sauraron karar ne ba tare da saka ranar dawowa ba saboda nadin da aka yi ma sa a matsayin alkali a kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa da na mambobin majalisar tarayya.

Tun a shekarar 2015 gwamnati ta kama El-Zakzaky tare da matar sa, Zeenat, biyo bayan wata kazamar arangama tsakanin mabiyansa da dakarun sojin Najeria a garin Zaria dake jihar Kaduna.

Rahotann sun bayyana cewar an kashe mabiya shi’a kimanin su 300 yayin artabu da dakarun sojin.

Ana tuhumar El-Zakzaky da matar sa da hada baki domin aikata kisa, taro ba bisa ka’ida ba, da tayar da tsugune tsaye da sauran su.

Da yake gana wa da manema labarai bayan yanke hukuncin kotun, Femi Falana, lauyan dake kare wadanda ake tuhuma, ya ce wadanda yake karewa basu samu damar bayyana a gaban kotu ba saboda yanayin rashin koshin lafiya da su ke ciki.

Ya ce tun ranar 14 g watan Disamba na shekarar 2015 da aka rufe su, ba a bawa lafiyar su kulawa ba, tare da bayyana cewar su na matukar bukatar a duba lafiyar su.

“Kotu ta daga sauraron karar su har sai baba ta-gani a daidai lokacin da su ke cikin tsananin bukatar a duba lafiyar su ,” a cewar Falana.

A ranar 22 ga watan Janairu na shekarar 2019 ne Jastis Kurada ya bawa gwamnatin Kaduna umarnin ta bawa El-Zakzaky da matar sa dama don a duba lafiyar su, umarnin da Falana ya ce gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here