Yan Kungiyar Asiri Sun Kashe Mutum 2 Masu Yiwa Kasa Hidima A Bayelsa

0
993

Musa Muhammad Kutama, Daga kalaba.

HUKUMAR ‘yan sandan jihar Bayelsa ta sanar da cewa wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar asiri ne a wani samamen daukar fansa da suka kai daya daga cikin gidajen da masu yiwa kasa hidima suke a Yenagoa sun kashe wasu mutum biyu dake aikin yiwa kasa hidima a Yenagoa jihar Bayelsa.

Wannan lamari ya faru a unguwar a Swali dake birnin Yenagoa a ranar larabar data gabata.

Da yake yin Allah wadai da al’amarin ‘yan kungiyar ta’adda, kwamishinan ‘yan sandan jihar Bayelsa Olusholla David, ya bayyana kaduwar sa game da kisan, kana ya bayar da tabbacin ci gaba da kare rayuwar
jama’a data sauran masu yiwa kasa hidima dake jihar.

Haka nan kuma gwamna seriake Dickson ya bayyana damuwarsa shima na kisan masu yiwa kasar hidima a jihar .

Ya zuwa rubuta wannan labari hukumar ‘yan sandan jihar Bayelsa bata bayar da sunayen wadan da aka kashe ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here