Matasan Jihar Kano Zasu Amfana Da Gwamnatin Ganduje – Mustapha Coach Gwarzo

  0
  1162
  Jabiru A Hassan, Daga Kano.

  JAGORAN matasa masu kare martabar dimokuradiyya da shugabanci nagari kwamared Mustapha Umar  Tallo Gwarzo, wanda akafi sani  da (Mustapha Coach), yace  Matasan jihar kano zasu amfana daga kyawawan shirye-shiryen gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje fiye da abin da aka yi masu a zangon farko cikin yardar Allah.

  Yayi wannan tsokaci ne  cikin hirar su da wakilin mu a garin Gwarzo, bayan bayyana sakamakon zaben gwamna da akayi, inda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sake samun nasara Karo na biyu, tareda sanar da cewa Matasan jihar kano suna goyon bayan gwamna Ganduje, sannan suna bukatar ci gaban jihar don haka be suka jajirce wajen ganin gwamnan ya sake lashe  zabe a Karo na biyu.

  Kwamared Mustapha Umar Tallo Gwarzo ya Kara da cewa lokaci yayi da matasa zasu fahimci dimokuradiyya da samar da ci gaba  ganin cewa nan gaba fa sune manyan wata rana, don  haka ne  ya kara yin Kira garesu dasu ci gaba da nuna kaunarsu da goyon bayan su ga gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta yadda zata cimma nasarori a wannan zango na shekaru hudu.

  Daga karshe, jagoran matasan yayi fatan alheri ga gwamna Ganduje da mataimakin sa da kuma dukkanin zababbu da suka sami nasarar zabukan da aka gudanar tun daga kan shugaban kasa Muhammadu Buhari har zuwa  sanatoci da yan majalisun tarayya dana dokoki a tutar jam’iyyar APC, tareda godewa matasa da sauran al’uma  da suka jajirce wajen tabbatar da cewa gwamna Ganduje shine  zai ci gaba da jagorancin jihar kano karo na biyu.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here