Ni Ne Na Cancanci Zama Shugaban Majalisar Wakilai Ta Tarayya – Alhassan Ado

  0
  1156

  Isah Ahmed, Daga Jos.

  Mai tsawatarwa na majalisar wakilai ta tarayya Alhaji Alhassan Ado Doguwa da ke  wakiltar mazabar Doguwa da Tudun Wada da ke Jihar Kano, yana daya daga cikin ‘yan majalisar da suka fito takarar neman shugabancin wannan majalisa.

  A wannan tattauna da ya yi da wakilinmu ya bayyana dalilansa na fitowa wannan takara, da kuma kudurinsa na ganin wannan  majalisa tayi biyayya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari,  sabanin majalisa mai wucewa.

  Ga yadda tattaunawar ta kasance

  GTK: Ganin majalisar wakilaita tarayya mai wucewa, an yi ta samun damuwa tsakaninta da shugaban kasa, a matsayinka na wanda ya sake cin zaben komawa wannan majalisa, ya ya kake ganin yadda wannan majalisa zata kasance a wannan karo?

  Alhassan Ado: To, ina son na tabbatar maka cewa ina daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayar tabbatar da mutumci da girman jam’iyyarmu ta APC a wannan majalisa, kuma ina tabbatar maka cewa ina daga cikin mutanen da suka yi kokarin ganin, an sami kyakyawar dangantaka tsakanin gwamnatin shugaba Buhari da wannan majalisa.

  Domin a lokacin da aka yi kokarin zaben shugabannin wannan majalisa  karo na 8, mune muka zabi shugabannin da jam’iyyarmu ta APC da shugaban kasa Buhari suka bayar da shawara a zaba, don a sami daidaito. Amma Allah cikin ikonsa aka sami wadansu daga cikinmu, suka hada baki da mutanen PDP aka zabawa majalisar shugabancin da ba shi ne shugabancin da jam’iyyarmu ta APC da Shugaba Buhari suka so a zaba ba.

  Wannan tarnaki da aka samu da matsalolin da aka rika samu wajen gudanarwa, ya zama wajibi a wannan karon mu dauki mataki mu dunkule mu fito da shugabancin da zai taimaki shugaban kasa Muhammadu Bauhari.

  GTK: Mane ne gaskiyar maganar da ake yi cewa kana daga cikin wadanda suke son zama shugaban wannan majalisa?

  Alhassan Ado: Babu shakka  ina son na  tabbatar maka cewa tun daga lokacin da aka sake zabena a matsayin dan majalisar wakilai ta tarayya, ina cikin wadanda suka fito takarar shugabancin wannan majalisa a wannan karo.

  Kuma dalila na fitowa takarar shugabancin wannan majalisa shi ne na yarda zan bayar da kyakyawar gudunmawa, don a sami zaman lafiya da aiki cikin lumana da natsuwa da daidaito, tsakanin majalisa da mai girma shugaba kasa Muhammadu Buhari. Kuma na yarda a matsayina na dan jam’iyyar APC, na fito daga jam’iyyar da take da rinjaye a wannan majalisa, wanda ya kamata a bata damar ta fitar da shugaban wannan majalisa, kuma na fito daga yankin da duk Najeriya babu yankin da ya fi shi ba jam’iyyar APC gudunmawa, Musamman wajen zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sannan kuma babu wani yanki da yafi wannan yanki ‘yan majalisar tarayya a Najeriya.

  Wannan yanki kuwa shi ne yankin Arewa maso yammacin Najeriya, yankin da ya hada jihohi guda 7, wato  Jigawa da Kebbi da Sakkwato da Zamfara da Katsina da Kaduna da kuma Kano.

  A Najeriya babu wani yanki da ya baiwa jam’iyyar APC gudunmawar kuru’u da goyan baya kamar wannan yanki. Albarkacin wannan yanki da na fito, ina ganin na dace na zama shugaban wannan majalisa.

  Na sani mutane zasu ce yaya mutumin da ya fito daga yankin da shugaban kasa ya fito, zai nemi shugaban majalisar wakilai ta tarayya tun da akwai tunanin da ake da shi na cewa jam’iyya zata fito da wani tsari, ma’ana kaso na mukamai da za a baiwa kowace shiya a Najeriya.

  Ina son in tabbatar maka cewa fitowa ta daga yankin da mai girma shugaban kasa ya fito, bai zai hana ni tsayawa takarar shugaban majalisar wakilai ba domin tsarin mulkin kasar nan, bai hana ba.

  Bayan haka idan har jam’iyya a lokacin majalisar nan ta 8,  bata ji kunyar tsayar da Femi Gbajabiamila ba daga jihar Legas, wajen da mataimakin shugaban kasa ya fito ba, duk da cewa ya sami akasi, bana tsammanin akwai son zuciya ko kuma abin kunya don ni da na fito daga Jihar Kano na nemi shugaban majalisar wakilai ta tarayya tun da shugaban kasa Buhari ba daga Jihar Kano yake ba.

  Bayan haka  a zauren majalisar nan, a yau babu dan majalisar da ya grime ni, kan aikin majalisa da kuma dadewa a cikin wannan majalisa.

  Domin a yanzu a zango na 9, da wannan majalisa zata shiga, zan shiga zango na 6 a wannan majalisa. Wannan ya bani damar da in magana ake yi ta gogewa da kwarewa da  tsarin aikin majalisa babu wanda ya wuce, ya zama shugaban wannan majalisa illa ni.

  Wannan ba na fada bane don na raina matsayin ‘yan uwana sauran ‘yan majalisa. Duk mutumin da yazo majalisa idan ya yi shekara guda a cikinta, ya yi gogewar da zai iya zama komai. Hatta sababbin ‘yan majalisa, doka ce kawai tayi masu sarkakiya cewa ba zasu iya zama shugaban majalisa ba.

  Amma a cikin sababbin ‘yan majalisa za a iya samun masu kwakwalwar da suka fi tawa. Za a iya samun masu ilmi da suka fi nawa, za a iya samun masu hikima da suka fi tawa, amma doka bata basu damar zama shugaban majalisa ba.

  Saboda haka idan ana maganar dadewa a majalisa ne nine na cancanci zama shugaban wannan majalisa. Amma ina son na tabbatar maka cewa wannan yunkuri da nake yi da wannan dama da nake da ita, da fitowa da nayi neman shugaban wannan majalisa,  ina mai biyayya  ga jam’iyya don ita ce uwata ita ce alkiblata.

  Idan yau jam’iyya tazo da wani tsari da ya saba da bukatata zan ajiye bukatata in yi biyayya ga bukatar jam’iyya. Amma abin da ya kamata mu gayawa jam’iyya shi ne tayi taka tsantsan duk abububuwan da zata yi, ta tabbatar tayi adalci ba son zuciya ba.  Ayi abin da  ko an zo an ajiyewa ‘yan majalisa zasu yarda cewa an shirya gaskiya.

  Domin duk matsalolin da ake samu wajen zabar shugabannin majalisa a Najeriya rashin adalci ne yake kawo su.

  Abin da yafi muni ma shi ne abin da ya faru wajen zaben shugabannin majalisa ta  8, aka zo aka sami wai shugaban majalisar dattijai dan jam’iyyar APC mataimakinsa dan jam’iyyar PDP.

  Ba a taba yin irin wannan hadin gambiza ba sai wannan lokaci kuma duk wannan abin ya taso ne sakamakon rashin gaskiya da rashin adalci da jam’iyya ta shimfidawa kanta karshe ‘yayan jam’iyyar suka bujire mata.

  Ni ban zabi Yakubu Dogara a matsayin shugaban majalisa ba. Mun yi abin da jam’iyya tace ayi ne. Mu kammu mun sani abin da jam’iyya ta ce ayi bai yi kama da adalci ba shi yasa ‘yan majalisa suka bijirewa jam’iyya suka zabi Yakubu Dogara.

  Karshe haka muka yi shekaru 4 nan kare ji biri jinni, haka muka yi zama irin na doya da manja. Bada hakkinmu ba ‘yan Najeriya suka rika kallonmu a matsayin masu tozarta shugaban kasa, suka rika kallonmu a matsayin mun bijirewa jam’iyya duk wadannan abubuwa sun faru ne a matsayin babu yadda zaka yi.

  Amma duk da haka tun daga lokacin da muka fara aiki da shugaba Buhari, har ya zuwa wannan lokaci. Mun yarda shugaba Buhari shugaba ne na kirki ingantatce, kuma mun yarda shugaba ne da jama’ar Najeriya suke kauna kuma sun yarda sun damka amana a hanunsa. Wannan yasa ko kana so ko baka so ya zama wajibi, indai kai wakilin jama’a ne kayi biyayya ga shugaba Buhari, kuma ka bashi goyan baya ya sami nasara kan manufofinsa da akidunsa na tabbatar da gaskiya da yaki da cin hanci da rashawa da inganta harkar tsaro da kokarin canza tattalin arzikin Najeriya ya koma mai amfani ga al’ummar Najeriya baki daya.

  Wannan ne yasa muke tare da shi kuma muna bada gudunmawa kan duk abin da yake yi.

  Tun da Allah ya taimakemu an sake zabarsa karo na biyu kuma ana magana ce ta alkibla kuma a ci gaba da wannan alkibla, to irinmu wadanda suka san daraja da mutumcin shugaba Buhari a zauren majalisa ya zama wajibi a tasa mu agaba mu shugabanci wannan majalisa domin ko babu komai a zauna lafiya, kuma a sami kyakyawan yanayi na aiki tsakanin shugaban kasa da bangaren majalisa.

  Ina son na tabbatarwa shugaba Muhammadu Buhari idan ya same ni a matsayin shugaban majalisar wakilai ta tarayya, to yaje yayi barci idonsa a rufe domin ya sami wanda zai rike masa amana da yi masa biyayya.

  GTK: Karshe wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya?

  Alhassan Ado: Ina kira ga ‘yan Najeriya mu yiwa Allah godiya kan yadda ya sake dawo mana da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin dawowar Buhari ba karamar albarka bace Allah ya yi mana.

  Muna rokon ‘yan Najeriya su taya shugaban kasa da addu’a kuma mu yiwa kasa addu’a domin a zauna lafiya a sami dorewar tattalin arzikin Najeriya.

  Irin barnar da mulkin jam’iyyar PDP tayi a kasar nan cikin shekaru 16, ba zai yuwu shugaba Buhari ya iya gyara wannan barna cikin shekaru hudu ba don ko shekaru hudun nan ma da aka kara masa bai zai iya gyarawa ba, amma na yarda zai dora kasar nan kan harsashin da zata ci gaba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here