An Kashe Mutane 4 A Fadan Kungiyoyin Asiri A Ribas

0
896

Musa Muhammad Kutana, Daga kalaba.

KIMANIN mutum hudu aka kashe a wani sabon fada da ya barke tsakanin yan kungoyoyin asiri biyu da basu ga maciji da juna a kauyukan Choba da Alakahia dake karamar hukumar Obio/Akpor jihar Ribas.

Bayanin da muka samu shi ne hargitsi ya barke ne tsakanin kungiyoyin biyu bayan da bangaren ‘yan kungiyar asiri ta choba suka tsinci gawar shugaban su kuma ba a san ko suwaye suka kashe shi ba wanda hakan ya sanya su kuma suka yunkura suka dauki fansa akan na Alakhahia.

Rikicin bai tsaya a nan ba jim kadan da yin wancan artabu tsakanin kungiyoyin biyu, yan kungiyar asiri ta choba suka kona duk gawarwakin wasu mutum uku da aka kashe akangon gini.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, DSP Nnamdi Omoni
,ya shaidawa wakilin mu cewa tabbas rikicin anyi shi kuma fada ne na ramuwar gayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here