Zamu Kalubalanci Zaben Gwamna Da Aka Yi A Kano – Dantakarar Gwamnan AGA

  0
  1268

  Jabiru A Hassan, Daga Kano.

  DAN takarar gwamnan jihar jihar Kano a karkashin  jam’iyyar All Grassroots Alliance watau AGA, Sheikh Tijjani Sani Auwal Darma ya bayyana cewar zasu ci gaba da kalubalantar zaben gwamna da aka yi a jihar kano har sai gaskiya ta fito fili.

  Dan takarar ya yi wannan bayanin ne a wata ganawar su da wakilin mu dangane da abubuwan da suka faru lokutan zaben da yadda aka bayyana gwamna mai ci a matsayin wanda ya lashe zaben, Inda ya sanar da cewa ko kadan, jam’iyyar AGA ba zata yi kasa a gwuiwa ba wajen ganin an sami gaskiyar lamarin.

  Sheikh Tijjani Sani Darma ya ce kowa dai yaga yadda zaben ya gudana, sannan anga yadda aka sanar da sakamakon zaben bayan sake jaddada zabuka a wasu kananan hukumomi 28, wanda  ko kadan babu adalci cikin wannan zabe, don haka ne jam’iyyar su ta AGA ta yanke shawarar kalubalantar lamarin ta fuskar shari’a.

  Daga karshe, dan takarar gwamnan ya yi fatan cewa kotunan da zasu gudanar da shari’ar zabe, zasu kasance adalai wajen ganin dimokuradiyyar Najeriya ta ci gaba da kasancewa cikin martaba da kima a idon duniya, Inda kuma ya bukaci dumbin magoya bayan su da zu ci gaba da kasancewa masu bin doka da son zaman lafiya kamar yadda suka saba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here