Gyaran Kananan Dam-dam Ya Kawo Ci  Gaba Ta Fuskar Tattalin arziki – Manoman Dam Din Kunnawa

  0
  1071

  Jabiru A Hassan, Daga  Kano.

  MANOMA da suka yi noman rani a dam din kunnawa sun bayyana cewa gyaran da aka yiwa kananan dam-dam dake fadin kasar nan ya kawo ci gaba ta fuskar tattalin arziki da samar da aikin yi ga dumbin al’umma.

  Jagoran manoman malam Muhammad mai albasa shi ne ya sanar da hakan a wata tattaunawa da suka yi da wakilin mu a dam din na Kunnawa, inda ya bayyana cewa kafin a gyara wannan dam na kunnawa ba’a yin komai a wajen, amma cikin ikon Allah bayan gyaran da aka yi masa an sami ingantuwar tattalin arziki ta fuskar noman  rani a wannan guri.

  Malam Muhammad mai albasa ya sanar da cewa gwamanatin shugaba Buhari tayi tunani mai kyau wajen bullo da shirin gyaran kananan madatsun ruwa domin tsugunar da makiyaya da kuma yin noman rani  ta yadda al’amura zasu kara bunkasa a kasa Baki daya.

  Manoman dake aiki a dam din Kunnawa sun yi roko ga gwamnatin tarayya data jihar kano da su kara fadada wannan madatsar ruwa tareda kyautata  gurin kiwo dake wannan dam domin ganin an cimma manufofin gyaran wannan dam mai tsohon tarihi.

  Daga  karshe, a madadin manoman dake  aiki a dam din Kunnawa dake  yankin karamar hukumar Dawakin Tofa  malam Muhammad mai albasa ya bada tabbacin cewa za’a ci gaba da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma dake wannan dam.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here