Majalisa Za Ta Kada Kuri’a Kan Kasafin Kudin 2019

0
641

Daga Rabo Haladu.

ANA sa ran ‘yan majalisar tarayya za su kada kuri’ar amincewa da kasafin kudin 2019 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar.

Tun a watan Disamba ne shugaban ya gabatar da kasafin da ya kai naira tiriliyan 8.83 ga majalisar dokokin kasa wanda aka saran majalisan ta amince da kasafin tun kafin lokacin zabukan da aka gudanar a Najeriya.

Ko da yake a baya majalisar ta ce dage zabe da aka yi ne ya shafi ayyukanta musamman amincewa da kasafin kudin 2019. Kasafin kudin shi ne na karshe a majalisar dokokin kasa ta takwas da za ta amince.

Kasafin kudin dai zai zama doka ne kawai idan ‘yan majalisar kasa suka amince da shi. Abin da kasafin 2019 ya kunsa

An tsara kasafin ne bisa hasashen Najeriya za ta fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu dari uku a ko wace rana.

Kuma an tsara kasafin ne bisa hasashen farashin danyen mai kan dala $60 kan ko wace ganga. Kuma kan farashin canji N305 kan dala daya.

Kasafin na Najeriya ya dogara ne da kudaden da kasar za ta samu daga albarkatun mai.

Game da wannan ne, Shugaba Buhari ya ce ya umurci kamfanin mai na kasar NNPC ya dauki dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da samun cimma burin fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu dari uku a kowace rana.

Shugaban ya ce kasafin kudin na 2019 na Naira tiriliyan 8.83 ya kunshi kudaden tallafi da kasar za ta samu biliyan N209.92.
Ma’aikatar cikin gida ce ta fi samun kaso mai yawa a kasafin kudin 2019 inda aka ware mata biliyan N569.07.

Ma’aikatar tsaro ce ta biyu, inda aka ware mata naira biliyan N435.62. Sai ma’aikatar ilimi da aka ware wa biliyan N462.24.
Ma’aikatar lafiya kuma an ware mata kudi ne naira biliyan N315.62.

An ware naira biliyan 45 ga shirin tallafawa yankin arewa maso gabas mai fama da rikicin Boko Haram da kuma naira biliyan 10 ga sabuwar hukumar raya yankin.

Haka kuma shugaba Buhari ya ce domin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a yankin Neja Delta an sake ware wa shirin afuwa na yankin naira biliyan 65 a kasafin na 2019.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here