Noman Auduga Zai Bunkasa A Kasar Najeriya – Sani Matazu

  0
  1322
  Mustapha Imrana Abdullahi, Daga Kaduna.
  SHUGABAN Kungiyar masu Noman Auduga tare da cinikinta na kasa reshen karamar hukumar Funtuwa Alhaji Malam Lawal Sani Matazu ya Kara jaddada aniyar Gwamnati domin taimakawa daukacin manoman Audugar a fadin kasa baki daya.
  Malam Lawal Sani Matazu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a kaduna lokacin da ya halarci taron kasuwar duniyar kasa da kasa da aka rufe a kwana nan.
  Sani Matazu ya ce idan aka dubu aniyar Gwamnatin tarayya na son taimakawa harkar Noma, a fili lamarin yake cewa Gwamnatin a shirye take ta Kara habbaka NOMAN Audugar da za ta wadaci kasa baki daya.
  Saboda haka sai ya bayar da tabbacin cewa a karamar hukumar Funtuwa za a ci gaba da samun ingantuwar al’amura a bangaren NOMAN Auduga da kuma dukkan sauran fannonin ayyukan Gona baki daya.
  ” Idan aka yi duba da kyau za a ga cewa Auduga tana daraja musamman ma idan an yi duba da yadda abin yake a can baya, amma a bana an samu farashin Auduga har ya kai naira dubu Dari biyu a matsayin Tan daya, Wanda hakan nasara ne babba”.
  Ya kuma shaidawa manema labarai cewa a matsayinsa na kantoman rikon karamar hukumar Funtuwa suna yin tsare tsaren taimakawa mata da matasa domin su koyi sana’o’i ta yadda za su dogara da kawunansu, kuma ana ba su horon koyon sana’ar ne a fannoni daban daban.
  Lawal Sani Matazu ya kuma yi Kira ga daukacin jama’a da su ci gaba da ba Gwamnati Mai ci a yanzu a dukkan matakin cikakken hadin kai da goyon baya domin ta yin hakan ne kwalliya za ta biya kudin sabulu.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here