Za’a Ci  Gaba Da Bunkasa Kasuwar Dawanau-inji Oyes

  0
  1716

  Jabiru A Hassan, Daga  Kano.

  WAKILIN  tashar kasuwar kayan abinci ta duniya dake Dawanau Malam Shehu Ali Oyes ya ce karamar hukumar Dawakin Tofa zata ci gaba da bunkasa wannan kasuwa ta yadda zata zamo  abar misali.

  Yayi wannan tsokaci ne a ganawar su da wakilin mu a ofishin sa, inda  kuma ya kara da cewa kasuwar Dawanau kasuwa ce  wadda ta ke da tsohon tarihi, sannan tana karbar baki daga sassa daban-daban na duniya, don haka  yace wajibi ne a bunkasa ta tare da inganta yanayin ta yadda zata ci  gaba da rike kambunta na kasuwar kayan  abinci ta duniya.

  Oyes ya ce  ko shakka babu shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai Kwa yana da bukatar ganin tattalin arzikin al’uma ya bunkasa, sannan yana son ganin kasuwanci da cinikayya suna habaka a kasuwar,  don  haka ne yake daukar matakai kyawawa na bunkasa kasuwar da kyautata yanayin ta kamar yadda ake gani a yau.

  Sannan ya bayyana cewa akwai dangantaka mai kyau tsakanin yan kasuwar ta Dawanau da hukumomin gudanar da kasuwar da masu tattara haraji, kana akwai fahimtar juna tsakanin shugabannin kungiyar kasuwar da shugabancin kasuwar wanda  hakan ta sanya al’amura ke tafiya cikin nasara a kasuwar.

  A karshe, Malam Shehu Ali Oyes, yayi amfani da wannan dama  India ya yi fatan alheri ga gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje bisa  nasarar da ya samu a zaben gwamna tareda taya murna da dukkanin wadanda suka  ci zabe a tutar jam’iyyar APC a kasa da jihar  kano  baki  daya, Inda kuma ya jaddada cewa zai ci gaba da jagoranci na adalci a wannan guri da yardan Ubangiji.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here