Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Kauyen Kaduna

0
1044

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WASU yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kuriga da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna inda suka tursasa mazauna kauyen tserewa daga garin.

Mazauna kauyen wanda mafi akasarinsu mata ne sun iso Birnin-Gwari da misalin karfe 3:30pm na ranar Laraba a matsayin yan gudun hijira.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi da wata kungiya ta saki ga manema labarai daga Birnin-Gwari.

“Yan fashi da makami sun kai hari kauyen Kuriga wanda ke hanyar babbar titin Birnin-Gwari-Kaduna sau tara.

“Harin baya-bayan nan da aka kai a daren ranar Talata ne inda aka sace mata da maza biyar sannan yan bindigan suka sace dabbobi,” kamar yadda yake a sanarwar.

“Muna bukatar dukkanin hukumomin tsaro da na kwararru da su kwana da shiri sannan su kawo dauki a wannan mumunan al’amari” inji kungiyar.

An tattaro cewa yan bindigar sun kuma aika wata wasika a yau (Alhamis) inda suka gargadi mutanen Kuriga da su bar yankin ko kuma a sace su.

Da aka kira kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo bai amsa sakon text da aka tura masa ba don jin yadda abun yake.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here