Zan Kara Himma Wajen Bunkasa Ilimi – Inji Alhaji Isyaku Gadar Zaura

0
904
Jabiru A Hassan, Daga  Kano.

WANI dan kasuwa kuma mai tallafawa harkar ilimi Alhaji Isyaku Gadar Zaura ya ce zai ci gaba da taimakawa fannin ilimi domin ganin an sami al’umma tagari.

Ya yi wannan bayani ne a hirar su da wakilin mu bayan kammala bikin yaye dalubai 31 na madarasatul Nurul Dinil Islam ta Gudau wanda aka gudanar ranar lahadin data gabata, tare da jaddada cewa yana dakyau al’umma su rika taimakawa ilimi domin shi ne gishirin zaman duniya.

Alhaji Isyaku ya kuma nunar da cewa baiwa yara ilimi tun daga tushe abu ne da zai baiwa yaran damar samun ingantaccen ilimi walau na addini ko na zamani, Inda kuma ya yi amfani da wannan dama wajen yabawa dukkanin wadanda suke da hannu wajen tabbatar da samun nasarar gudanar da wannan sauka cikin nasara.

Daga karshe, ya yi godiya ta musamman ga gwamnan jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda aiyukan alheri da yake yiwa jihar, ciki har da hanyar da ta tashi daga masallacin kunture zuwa Yar Gudau ta wuce Zaura zuwa Ganduje kana ta hade da babban titin zuwa Dambatta domin amfanin al’ummar wadannan yankuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here