Mai Gadi Ya Zabi A Gina Tuka-Tuka A Kauyensu A Kan Karbar Kyautar Gida

0
839

Daga Usman Nasidi.

WANI mai gadi ya bukaci mai gidan sa ya rike kyuatar gidan da ya bashi a matsayin sallama tare da mika bukatar a haka rijiyar tuka-tuka a kauyensu.

Mai gadin, Musa Usman, ya fito ne daga kauyen Giljimmi da ke karkashin karamar hukumar Birniwa a jihar Jigawa.

Wani dan asalin kasar Indiya ne ya so bawa Musa kyautar gida a matsayin sallamar aikin da ya dade yana yi masa a matsayin mai gadi, amma sai ya nemi mai gidan nasa ya gina musu rijiyar tuka-tuka a kauyensu.

Lamarin ya faru ne yayin da Musa zai dawo kauyensu bayan ya yi aiki a matsayin mai gadin manajan kamfanin magunguna na ‘Jawa International Limited’ a jihar Legas na tsawon shekaru 25.

Manajan kamfanin, Mista V. Verghese, ya yanke shawarar gina wa Musa gida domin nuna jin dadin aikin da ya yi masa a matsayin mai gadi.

Amma saboda matsanancin halin wuyar ruwa da kauyensu ke ciki, sai Musa ya nemi a bar maganar gina masa gida, a gina rijiyar tuka-tuka da jama’a zasu amfana.

Kafin ginin rijiyar da Musa ya nema a wurin mai gidansa, mutanen kauyensa na yin tafiya mai nisan gaske kafin su samo ruwan sha mai tsafta.

A jawabinsa, Musa ya yi godiya ga Mista Verghese bisa aikin alherin da ya yi a kauyensu, ya ce ko kadan ba ya nadamar kin karbar kyautar gidan da ya yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here