An Sace Shugaban Hukumar UBEC Tare Da Diyar Sa A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

0
635

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

SHUGABAN hukumar kula da ilimin bai daya (UBEC), Mohammed Abubakar, na daga cikin dumbin mutane da ‘yan bindiga suka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Litinin da rana.

Wata majiya dake da kusanci da Abubakar ta shaida wa majiyar mu cewar an sace shi ne tare da diyar sa a hanyar su ta zuwa Abuja.

Rahotannin sun bayyana cewar masu garkuwa da mutanen sun harbe direbansa, wanda nan take ya mutu.

“Da gaske ne an sace shi tare da diyar sa a hanyar su ta tafiya Abuja. Sun harbe direbansa, kuma nan ta ke ya mutu ,” a cewar shaidar da bai yarda a ambaci sunansa ba.

Wani shaidar gani da ido, Mohammed Dambatta, wanda ya sha da kyar, ya shaida wa majiyar jaridar mu cewar masu garkuwa da mutanen sun sace mutane da dama a daidai Kurmin Kare a karamar hukumar Kachia dake jihar Kaduna da misalin karfe 3:00 na ranar Litinin.

A cewar sa, masu garkuwa da mutanen sun yi harbin iska a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, lamarin da ya saka a kalla motoci 15 suka tsaya, wanda hakan ya bawa masu garkuwa da mutanen damar tafiya da mutane da dama zuwa cikin daji.

“Na kidaya a kalla motoci 15 wadanda aka sace mutanen ciki, a cikin motocin har da ta ‘yan sanda da motar safarar mutane mallakar gwamnatin jihar Kano (Kano Line) da kuma wata mota kirar ‘Jeep’ ,” a cewar sa.

A satin da ya gabata ne babban sufeton rundunar ‘yan sanda na kasa (IGP), Abubakar Adamu, ya bayyana cewar hanyar Abuja zuwa Kaduna tayi lafiya bayan kaddamar da wani atisaye mai taken ‘Puff Arder’ domin yaki da miyagun aiyukan, musamman matsalar sace matafiya a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here