Buhari Ya Bada Umarnin Sakin ‘Yan Najeriya 3 Da Hukumar Saudiyya Ta Kama

0
696

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya tabbatar da cewar hukumomin kasar Saudiyya sun saki matashiyar nan yar Najeriya, Zainab Aliyu, da aka yi kuskuren kama wa bisa zargin laifin safarar kwaya.

Hukumomin kasar Saudiyya sun kama Zainab, daliba a jami’ar Maitama Sule dake Kano, a ranar 26 ga watan Disamba na shekarar 2018 bisa zarginta da shiga da jaka dauke da kwayar ‘tramol’ zuwa kasar Saudiyya.

Matashiyar ta tashi zuwa kasar Sauddiya daga filin jirgin sama na Mallam Aminu domin gudanar da aikin ‘umra’ tare da mahaifiyarta, Maryam, da ‘yar uwarta, Hajara.

Babbar mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren harkokin da suka shafi kasashen waje, Abike Dabiri Erewa, ce ta sanar da umarni da shugaba Buhari ya bayar a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, ta kara da cewa tuni gwamnatin tarayya ta fara tattauna batun sakin Zainab tare da wasu mutane biyu dake da irin matsalar da Zainab ta samu.

“Shugaban kasa Muhammadu Buharu ya umarci ministan shari’a ya dauki matakan da suka dace a kan matsalar matashiyar. Mun fara tattauna wa da hukumomin kasa, za ta dawo gida tare da wasu mutane biyu dake da irin wannan matsala ,” kamar yadda Dabiri ta sanar a shafinta na Tuwita.

Mahaifin Zainab ne ya fara rubuta wata takardar korafi da ya aika wa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a kan zargin cewar an saka kwaya a jakar diyar sa.

Daga bisani, binciken NDLEA ya gano cewar akwai gungun wasu ma’aikatan kamfanonin jirgin sama da suka kware wajen yin cushen kwayoyi a jakankunan matafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here