An Sace Surukin Dogarin Shugaban Kasa Buhari

0
1252

Daga Usman Nasidi.

RAHITANNI da muke samu na bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Daura a jihar Katsina – wato mahaifar Shugaban kasar Najeriya inda aka sace surukin Dogarin shugaba Buhari a ranar laraba.

Sarkin mahaifi ne ga Hajiya Fatima Musa, mai dakin Kanal Muhammad Abubakar, babban dogari ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun yi harbe-harben bindiga domin fatattakar mutane kafin su arce da Sarakin a mota kirar Peugeot 406.

Shugaban karamar hukumar Daura na riko Injiniya Abba Mato ya shaida wa manema labarai cewa bayan sallar magriba ne maharan suka kaiwa garin farmaki.

Ya kuma ce sun sace surukin dogarin Shugaba Buhari, wato Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar.

Har ila yau a ranar Laraban ne aka yi jana’izar mutane sha hudu wadanda suka mutu sanadiyyar wani harin da wasu mahara suka kai karamar hukumar Safana shi ma dake jihar Katsina.

Dan majalisar dokokin yankin a majalisar jihar Katsina, Honorabul Abduljalal Haruna Runka, ya shaida cewa maharan sun kai farmaki ne a kauyen Gobirawa da kuma Shaka Fito.

Hakazalika dan majalisar ya ce maharan sun sace mata da wasu daga yankin karamar hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here