
A duk lokacin da kungiya mai zaman kanta ta Shiga rudanin shugabanci akan sami tsaiko da rashin tabbas da rashin mutun ta juna da kuma rarrabuwar kawunan yayan kungiya domin kowane bangare yana ikirarin cewa shine halastaccen jagora.

kuma a mafiya yawan lokuta, rabuwar kawuna a kungiya musamman irin ta manoma, domin sau tari ana rasa wasu abubuwa masu amfani ga manoma walau daga gwamnatin tarayya ko cibiyoyin bincike kan noma ko gwamnatin jiha kodai wata babbar kungiya ta manoma ta duniya kamar yadda ake gani yanzu a jihar kano.
Sannan kusan dukkanin mambobin kungiyoyin da suke da irin wannan Matsala ta rikicin shugabanci, suna rasa sahihin tsari na yadda zasu amfani wannan kungiya domin kowane bangare yana bugun kirji cewa shine mai ikon tafiyar da kungiya.
Wani dogon bincike da na gudanar kan kungiyar manoma ta kasa reshen jihar kano watau AFAN, na fahimci cewa kungiyar ta rabu gida biyu watau akwai bangaren da gwamnati ke tafiya da shi karkashin shugabancin Alhaji Farouk Rabiu da kuma bangaren da uwar kungiyar ta AFAN ta kasa ke tafiya dashi wanda Alhaji Abdulrashid Magaji Rimin Gado ke shugabanta.
Bugu da kari, nayi duba a hankali cewa bangaren Farouk Rabiu shine bangaren da gwamnati ke tafiya dashi domin kusan dukkanin abubuwan da akeyi kuma wadanda suka shafi manoma anayi ne da wannan bangare kuma shine bangaren da mataimakin gwamnan kano kuma kwamishinan gona Dokta Nasiru Gawuna ke Hulda dashi kai tsaye.
Ita kuma uwar kungiya ta AFAN ta kasa tana aiki ne kai tsaye da bangaren Abdulrashid Magaji Rimin Gado batare da wancan bangare na su Farouk Rabiu ba, wanda idan aka dubi wannan lamari, ko shakka babu manoman jihar kano suna cikin rashin tabbas a shugabancin kungiyar su tun lokaci mai tsawo.
A cikin tattaunawa da nayi da wasu daga cikin manoman jihar kano, mafiya yawan su sun bayyana cewa muddin ba’a shiga an kawo karshen wannan dambarwa ta shugabanci ba, to lallai manoma sai dai su ci gaba da hakurin tafiya cikin wannan yanayi mai cike da sarkakiyar gaske.
Anan yana dakyau maigirma mataimakin gwamna kuma kwamishinan gona na jihar kano da it’s kanta uwar kungiyar ta AFAN ta kasa su gaggauta haduwa domin kawo karshen wannan rabuwar kawuna a harkar kungiyar manoma domin a matsayin sa na shugaba kuma jagora, bazai ji dadi ba a ce jihar sa tana cikin dambarwa iron ta shugabancin kungiyar manoma ta AFAN.
Aikin hade kan kungiyar AFAN mai sauki ne idan har bangaren gwamnatin kano dana uwar kungiya suka hadu suka daidaita tsakanin bangarorin biyu ta yadda manoman jihar kano zasu amfani hadin kan da suke yi a kungiyance, sannan na shirya tsaf domin jin sahihancin kowane bangare ta yadda za’a fahimci yadda lamarin shugabancin wannan kungiya ta AFAN ya sami rashin daidaito.
Ga masu Karin haske ko wani bayani mai amfani sai a tuntubi:
Jabiru A Hassan, Wakilin jaridun New Nigerian da Gaskiya Tafi Kwabi a Jihar Kano a kan wannan lambar waya: 08039640882 ko adireshin yanar gizo. jabiru.hassan@yahoo.com