A Zabi Sanata Kabiru Gaya Domin Ci Gaban Kasa Baki Daya

  0
  1098

  Mustapha Imrana Abdullahi, Daga kaduna.

  AN bayyana zaben sanata Kabiru Ibrahim Gaya a matsayin Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa da cewa ita ce hanya mafita ga daukacin Najeriya da nahiyar Afirka baki daya.

  An dai bayyana cewa in har yayan jam’iyyar APC da kuma al’ummar Najeriya basa son maimata irin abin da ya faru a dauko wani da ba dan APC ba ya zama Mataimakin shugaban kasa dole ne ayi hattara a zabi sanata Kabiru Ibrahim Gaya a matsayin mafita ga kowa.

  Wata Kungiyar mai suna Arewa APC Solidarity Forum (AASF) da ke kare muradun APC ce ta bayyana hakan inda Kungiyar ta Kara yin Kira ga jam’iyyar APC da yayanta su hada Kansu su kuma gyara gidansu domin kada garin gyaran gira a rasa idanu.

  Kungiyar ta ci gaba da cewa tabbatar da Kabiru Gaya a matsayin mataimakin shugaban majalisar Dattawa ta Tara domin hakan zai Hana sake maimata kuskuren da aka yi na wani can daban ya zama mataimaki kamar yadda aka yi a Majalisar ta Takwas hakika ita ce hanya mafita ga APC tare da yayanta baki daya.

  Shugaban wannan kungiya kwamared Bulama Abdulrahman ne ya yi wannan jiran a wajen wani taron manema labarai da kasancewa sanata Kabiru Ibrahim Gaya a matsayin mutum da ya dage wajen ganin Nijeriya ta ci gaba, ko a kwana nan irin yadda Sanata Kabiru Gaya ya dage wajen ganin an kubutar da yar makarantar da ke karatu a jami’ar Maitama sule da ke Kano bayan da aka rike ta a kasar Saudiyya bayan da hukumomin kasar Suka tsare ta bisa zargin laifin shiga da haramtattun kwayoyi kasar lallai abin a yana ne.

  Kwamared Bulama ya ci gaba da cewa irin yadda tsohon Gwamnan Kano sanata Kabiru Gaya ya gabatar da bayanin a gaban majalisa irin yadda dalibar ta samu Kanta lallai abin a yana ne Wanda hakan ya jagoranci fitowar dalibar Zainab Yusuf, don haka ya zama wajibi a ci gaba da bashi hadin kai da goyon baya ta yadda kasa da al’ummarta baki daya kowa zai amfana.

  Kuma kokarin da sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya yi domin ganin an saki Zainab ba wai na Ita kawai bane kawai har ma da na ganin an saki wani mutum Mai suna Ibrahim Abubakar Dan shekaru arba’in da biyar da ya samu kansa kamar Zainab inda wasu marasa kishi Suka Saka masa kwaya a cikin kayansa.

  “Sakamakon hakan yasa sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya yi kokarin gudanar da bincike na kashin kansa a game da lamarin kuma an ya gano cewa Babu wani laifin hadahadar kwayoyin da mutanen Suka aikata, hasalima tuni aka kama mutane shida kuma suna can suna fuskantar shari’a duk a kokarin da sanata Kabiru Gaya ya yi na ganin an tabbatar da gaskiya da adalci ga kowa.

  Hakika yanzu lokaci ne da za a bayar da dama ga masu son kasa tare da jama’ar ta baki daya su amfana.

  Shugaban Kungiyar ta AASF ya Kara fadakar da jama’a cewa kokarin sanatan na bukatar a talkafa masa domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu ga Nijeriya da nahiyar Afirka baki daya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here