Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Kafa Masarautu 4 A Jihar Kano

1
1583

Daga Usman Nasidi.

MAJALISAR dokokin jihar Kano karkashin jagorancin kakakin majalisar Rt. Hon Alhassan Rurum ta amince da kafa sababbin masarautu guda hudu a fadin jihar Kano.

“Ba a samu wadanda suka nuna rashin amincewar su ba a dakin majalisar. Sai dai akwai wadanda suka dinga fita daga majalisar wadanda alamu ke nuna cewa ba su ji dadin dokar ba,” wani dan majalisar wanda ya bukaci a boye sunansa, ya bayyanawa manema labarai cewa.

“Gwamnan jihar ya na so ya rage darajar sarkin Kano, Sanusi Lamido a idon duniya, shi ne ya sanya ya ke so ya kirkiri masarautun guda hudu ya sanya su a matsayi daya da sarkin Kanon.”

Garuruwan da dokar ta yadda su yi sarautar sun hada da Masarautar Kano, Masarautar Rano, Masarautar Gaya, Masarautar Karaye da kuma Masarautar Bichi.

A yanzu haka dai ana shirin mika dokar wajen Mai Girma Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje domin ya rattaba hannu akan dokar wacce za ta share hanya akan nadin sababbin sarakunan Kanon na yanka.

A jiya ne gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, ya sanya hannu akan dokar da aka gabatar da ita gareshi.

Ganduje ya bayyana hakan yau Larabar nan a wata hira da yayi da manema labarai a gidan gwamnatin jihar Kano.

“Mun samu labarin dokar da aka aikawa gidan gwamnatin jihar Kano, inda aka bukaci ta sanya hannu a dokar kafa sababbin masarautun yanka guda hudu a jihar nan.

“Muna fatan wadanda suka bukaci hakan sun bukaci hakan da zuciya daya ne. Kuma muna fatan sunyi hakan da niyyar samun ci gaba ga jihar Kano baki daya,” in ji Ganduje.

Mai Girma Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar kafa sabbin masarautu guda hudu (4) da suka hada da Rano, Karaye, Gaya da Bichi.

Bayan saka hannu a kan wannan sabuwar doka, gwamnatin Jihar Kano zata nada sabbin sarakuna na wannan masarautun hudu da kuma zana iya fadin kasar su, sannan kuma shi Sarkin Kano na yanzu Mallam Muhammadu Sanusi II zai zama Sabon Sarkin Birnin Kano da Kewaye.

Sarkin Birni da Kewaye na da kananen hukumomi guda 10 a karkashin sa da suka hada da
1- Kano Municipal
2- Fagge
3- Nasarawa
4- Gwale
5- Tarauni
6- Dala
7- Minjinir
8- Ungogo
9- Kumbotso
10- Dawakin Kudu

Sarkin Rano kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;
1- Rano
2- Bunkure
3- Takai
4- Kibiya
5- Sumaila
6- Doguwa
7- Kiru
8- Bebeji
9- Kura
10- Tudun Wada

Sarkin Gaya kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;
1.Gaya
2.Ajingi
3.Albasu
4.Wudil
5.Garko
6.Warawa
7.Gezawa
8.Gabasawa

Sarkin Bichi kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;
1- Bichi
2- Bagwai
3- Shanono
4- Tsanyawa
5- Kunci
6- Makoda
7- Danbatta
8- Dawakin Tofa
9- Tofa

Sarkin Karaye kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;
1- Karaye
2- Rogo
3- Gwarzo
4- Madobi
5- Kano
6- Rimin Gado
7- Garun Mallam

Sarkin Birnin Kano da Kewaye Mallam Muhammadu Sanusi II shine zai zamu Shugaban majalisar zartarwa na Masarautun guda biyar, sannan kuma Sarkin Rano shi zai zama mataimakin sa.

Sannan shugabancin wannan majalisar zai zamu na karba karba ne wato rotational inda kowanne shugaba zai shekara biyu inda bayan kammalawar waainda sa kuma gwamnatin jiha na da hurumin kara masa wani waadin karo na biyu.

Sannan sauran yan majalisar masarautar sun hada da
1- Sakataren Gwamnatin Jiha
2- Kwamishinan Kananen Hukumomi
3- Ciyamomin Mulki na kananen hukumomin
4- Hakimai masu nada Sarki bibiyu saga kowacce Masarauta.
5- Wakilcin mutum 5 da Gwamna zai nada.

Daga karshe kuma sabuwar dokar bata hana wani wanda ya gaji Sarautar Kano daga sauran sababbin masarautun guda hudu ba, zama Sarkin Birnin Kano da Kewaye indai har sun gada.

A satin da ya gabata ne dai gwamnatin jihar Kanon a karkashin gwamnan jihar Dakta. Abdullahi Umar Ganduje ta fara shawara akan yadda za ta kafa doka wacce za ta bata damar kafa masarautun yanka guda hudu a fadin jihar.

Hakan bai yiwa mutane da yawa dadi ba musamman ma Sarkin Kano Muhammad Sanusi na II, wanda shi ne za a yiwa kishiya.

To sai dai ba a san ainahin wainar da ake toyawa ba a cikin fadar jihar Kanon, domin kuwa tun lokacin da aka fara maganar kafa masarautun jihar har yanzu fadar jihar ba ta ce komai akan hakan ba.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here