Masari Ya Share Mana Hawaye – Kantoman Riko Anas Isa

0
921
Mustapha Imrana Abdullahi.
AN bayyana Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari a matsayin mutumin da al’ummar karamar hukumar kankara ke alfahari da shi.
Kantoman rikon karamar hukumar Alhaji Anas Isa kankara ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kankara.
Alhaji Anas Isa, ya ci gaba da bayanin cewa akwai hanyar da ta tashi daga garin kankara zuwa Dan Sabau da ake yin amfani da hanyar a kalla shekaru sittin da suka gabata, an yi ta hakilon yadda za’ a yi wannan hanya amma abin ya gagara sai a lokacin Masari a yanzu da yake Gwamnan Katsina ana nan aikin hanyar  sai dai karashe kawai.
“Akan wannan hanya, mutanen da suka gabata sun je sun ga duk wanda yakamata su gani, amma ta gagara wadansu da suka gabata duk sun yi ta kai komo ayi wannan hanya saboda muhimmancinta musamman wajen fitar da amfanin Gona amma lamarin ya gagara, sai kawai ga Gwamnan jama’a Alhaji Aminu Bello Masari da a kullum tunaninsa yaya za a taimakawa mutanen karkara, a yanzu wannan hanya Mai shekaru Sittin ta zama Daura karasa wa kawai don haka muna godiya da garin ciki”.
Ga kuma wata hanyar da ta tashi zuwa irin su wawal kaza, Tuge har zuwa Dayi da ta ratsa garuruwa da dama ana nan ana yin aikin.
Sai kuma aikin Dam domin jama’a su samu ruwa duk ana ta ayyukan don haka tsakanin mu da Gwamna Aminu Bello Masari hakika sai godiya da addu’ar alkairi.
Kantoman Kankara Anas Isa, ya Kara da cewa ko a cikin garin Kankara a can baya inda aka wuto ramukan hanya sai dai mutum ya zabi inda zai jefa kafarsa idan yana tafiya amma a yanzu ana ta ayyukan Samar da ingantattun tituna.
Hakazalika Alan lamarin tsaro nan ma Masari na yin bakin kokarinsa domin ganin komai ya ta fi dai dai, saboda jama’ar karamar hukumar Kankara na sane da irin ayyukan da Ake yi ba dare ba Rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here