Kabilar Nba Na Kasuwancin Bani Gishiri In Baka Manda A Kurus Ribas

0
988

Musa Muhammad kutama, Daga kalaba.

DUK da kasancewar an samu wayewa ta zamani da kuma kudi na kasa da
Najeriya tayi bayan ta samu mulkin kai a 1960, bayan shekara 63  har yanzu wasu al’ummomi dake sassan kasar Najeriya na yin al’adar nan ta cinikin bani-gishir-in baka manda wanda a shekaru masu yawan gaske aka rika gudanar da wannan ma’amala ta kudi ta hanyar cinikaiya a kasar nan.

KASUWAR Da AKE CINIKIN BANI GISHIRI IN BAKA MANDA

A jihar kuros riba mai cike da al’adu da dabi’un mutane kala-kala, har yanzu akwai wata al’umma a wata kasuwa dake karamar hukumar Akpabuyo wacce kasuwace zalla da ake yin cinikin bani gishiri-in –baka manda wanda ko a shekarun baya ma mun taba bayar da labarin wannan kasuwa ganin cewa ana mulki na demokradiyya ne ko
lamarin ya sauya an bar nau’in wancan kasuwaci da kuma ciniki ashe har yau har gobe ana nan ana cin wannan kasuwa.

A wannan karo wakilin mu, a sake leka kasuwar ta Esuk Mba dake karamar hukumar Akpabuyo inda wadannan al’umma ke ci gaba da kasuwancin su na bani gishiri in baka manda inda wannan kasuwa ke ci kowace asabar kuma tana da kaiyadadden lokaci na tsawon sao’i biyar kacal wato daga karfe bakwai na safiya zuwa karfe sha biyu na rana kowace asabar.

KAYA A KASUWAR

Kayaiyakin da ake sayarwa a kasuwar sun hada da kifi, Doya, Gishiri, Garin kwaki, fulawa, Maggi dunkule, Danye da busasshen kifi, kaji da kuma naman shanu sauran sune manja, man gyada, tumatiri, tattasai da kuma sabulun wanka dana dauraya.

Yadda ake cin kasuwar kuwa shi ne mabukacin manja zaije kasuwar ce da Doyarsa kwara hudu sai ya nemi mai sayar da manja ya bashi Doyar shi kuma ya karbi galan na manja.Ga wanda yake son sabulun wanka ko na dauraya shi kuma maggi dunkule yake bayarwa sai a bashi sabulan kana kuma wanda yake son a bashi kifi shi kuma kaji yake bayarwa amma ya danganta da kimar irin kazar da yaje da ita.

Kudi dai basu da wani tasiri a kasuwar domin ma idan mutum yaje da kukinsa a hannu haka zai dawo dasu koda kuwa abinci mutum zaici sai ya nemi masu ganyen miya ya basu gari su kuma su bashi nau’in irin abincin da yake bukata ko su bada ya’yan su mata jingina su karbi kayan abinci.

Wannan kasuwa  dai ta samu asali ne a shekarar 1956, tun daga lokacin da turawa suka yi wa kasashen Najeriya mulkin mallaka kuma wata cibiya ce ta saye da sayar da bayi ana ketarawa dasu zuwa sauran sassan nahiyar turai a wancan lokaci.

Shugabar kasuwar Ekaette Asuquo ta shaidawa wakilin mu cewa wannan kasuwa “mun gaje ta ga iyaye da kakanni tun lokacin da turawa suka zo yankin nan suka mamaye sukayi mulkin mallaka tsawon shekaru sukayi suka tafi suka bar mana gadonta don har yanzu akwai sauran irin ginin da sukayi suka tafi suka bar mana tun daga wancan lokaci 1956, kana suka kafa kasuwar har suka tafi muma muka gada wurin namu iyayen don haka ake ta yin wannan kasuwanci na bani gishiri.

Wata ‘yar kasuwa Emem Enohda ta saba cin waccan kasuwa tace “ko da wasa bazan  taba bari cin waccan kasuwa ya wuce ni ba “tab ai nabar ciniki da samun kudi ya wuce ni idan nayi fashin zuwa kasuwar don haka babu makon da bana zuwa cin waccan kasuwa”inji Emem.

Kafin wakilin mu ya baro kasuwar yaga dimbin mabukata ‘yan kauye na kwarara zuwa kasuwar kuma kowa ba kuki yake rikowa ba face irin nau’in abinda yake so ya bayar musaya a bashi wanda yake so.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here