Kwana 1 Da Haihuwa: Ta Sayar Da Jaririnta Kan Naira Dubu 600 Don Sayen Wayar Salula

0
930

Musa Muhammad kutama, Daga kalaba.

SASHEN rundunar ‘yan sandan jihar Imo dake yaki da masu aikata fashi da makami ta ce ta kama wata mata mai suna Nneka Donatus, mai kimanin shekara 27 da haihuwa bisa zarginta da laifin sayar da jaririyarta ‘yar kwana daya da haihuwa ta  a kauyen Ezinachi dake karamar hukumar Okigwe jihar Imo.

Uwargida Donatus da abokan huldar ta  Ujunwa Udechukwu dake aiki a ma’iakatar harkoki da walwala ta mata mai shekara 40 da haihuwa da kuma Nneoma Onwusereaka shekara 37 sun hada baki da uwar yarinyar su suka sayarwa wasu ma’aurata dake neman haihuwa basu samu ba.

‘Yan sanda sun sanar da cewa wadda ake zargi da yunkurin sayar da jaririyarta ta gayawa ‘yan sanda cewa tayi haka ne domin ta sayi wayar salula da kudin kana sauran canjin kuma ta sayi zannuwa dasu.

Nneka Donatus ta shaidawa manema labarai a harabar ofishin ‘yan sandan jihar Imo dake Owerri ce wa “ na sayi wayar salula ne da kudin wasu kuma na sayi zannuwa dasu da kuma takalman sanyawa, dama ni  burina idan na haihu lafiya in sayar da abinda na haifa domin ni bani da niyyar rike abinda na haifa don ina laifi ‘ya’ya biyar nake dasu duk da wanda na sayar  cikon na shida ” in jita

Nneka matar da ta sayar da ‘yarta tace bayan ta sayar da ‘yata kan kudi naira dubu dari shida, tayi amfani da dubu 15 kana sayi wayar salula zannuwa, takalman sauran canjin na shiga mota na dawo gida inda ts kirga wasu kudin ta ba Nneoma Onwusereka ragowar kudin domin su fara kasuwanci dashi.

Mijin matar da aka ce an basu kudi suyi
sana’a yace shidai yasan an bashi naira dubu 10 cikin kudin saboda rawar da ya taka wajen sayar da jaririyar amma ba wasu kudin azo agani aka bashi ba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Rabi’u Ladodo ya tabbatarwa manema labarai da afkuwar hakan kana yace ana nan ana binciken su kuma da zarar sun gama bincike kotu za’a tura su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here