Kotu Ta Bayar Da Umarnin A Kamo Hadiza Gabon Cikin Awanni 24

0
2146

Daga Usman Nasidi.

A RANAR Alhamis ne wata wata kotun Majistare a Kano karkashin Alkali Muntari Gambo ta bayar da umurnin a kamo fitaciyyar jarumar Kanywood, Hadiza Gabon saboda rashin amsa gayyatar kotu.

Jarumi Mustapha Naburaska ne ya shigar da kara a kotu kan zargin cin zarafinsa da barazana da ya ce da Hadiza Gabon din ta yi masa.

Rahotanni sun bayyana cewa Naburaska ya shigar da kara a kotu ne kai tsaye saboda yana fargabar ‘yan sanda ba za su dauki mataki a kan ta ba.

“Ka san cewa Hadiza Gabon tayi suna kuma tana da abokai musamman cikin ‘yan sanda da manyan ‘yan siyasa,” inji wata majiya daga Kannywood.

Alkalin kotun Majistare da ke Muntari Dandago ya umurci kwamishinan ‘yan sanda na Kano, Muhammad Wakili wanda akafi sani da Singham ya kamo jarumar tunda ya ki amsa gayyatar kotu.

“Tunda wacce aka yi kara ba ta da shirin amsa gayyatar kotu, Ina umurtar kwamishinan ‘yan sanda ya sanya a kamo wacce aka gayyata kotun.

“Ina kuma umurtan kwamishinan ‘yan sandan ya gudanar da bincike kan zargin da mai shigar da kara ya yi idan an samu gaskiya ciki sai a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya domin ta fuskanci shari’a.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here