Ku Daina Cin Shinkafar Waje, Akwai Guba A Cikin Ta – Hameed Ali

0
515

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN hukumar hana fasa kwabri ta kasa da aka fi kira da ‘Kwastam’, Kanal Hameed Ali (mai ritaya), ya roki ‘yan Najeriya a kan su daina cin shinkafar da aka shigo da ita daga kasashen waje saboda akwai guba a cikin ta.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi a wurin wani taro da ma’aikatar kudi ta shirya a Abuja.

Ali ya ce gwamnatin tarayya ba ta bayar da lasisin shigo da shinkafa ga kowa ba, a saboda haka duk shinkafar kasar waje da aka gani a Najeriya an shigo da ita ne ta barauniyar hanya.

Shugaban na Kwastam ya ce dukkan shinkafar da aka shigo da ita Najeriya na dauke da guba, saboda ta shafe a kalla shekara biyar a cikin rumbu.

“Akwai sinadari mai guba da ake zuba wa cikin shinkafar dake cikin rumbu don kar ta lalace.

“Sannan ana canja wa shinkafar buhu tare da canja kwanan wata don mu dauka sabuwa ce, hakan yasa muke kamuwa da cututtuka sakamakon cin irin wannan shinkafa.

“Ina rokon ‘yan Najeriya da su daina cin shinkafar kasar waje, mu ci tamu ta gida don mu zauna lafiya mu kuma taimaka wa hukumar kwastam wajen hana kasuwancin shinkafar waje, ” a cewar Ali.

Kazalika, ya bayyana cewar batun safarar shinkafar waje na daya daga cikin manyan kalubalen da jami’an kwastam ke fuskanta, ya kara da cewa ana cigaba da safarar shinkafar ne saboda har yanzu ana amfani da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here